Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-21 17:17:58    
An kammala gina katafaren dandalin wasan kwaikwayo na kasar Sin da kuma soma nuna wasanni

cri

Katafaren dandalin wasan kwaikwayo na kasar Sin shi ne babban ginin al'adu da ke da alamar kasar Sin wadda ta zuba jari wajen ginawa don fuskantar karni na 21. Kammala gina dandalin nan da kuma yin gwajin nuna wasanni a cikinsa ya jawo hankulan mutane sosai.

Lokacin da ake nuna wasan, lokaci ne da ya yi daidai da ranar bikin gargajiyar kasar Sin , wato bikin gargajiyar kasar Sin na haduwar iyali, ma'aikatan ginawar katafaren dandalin wasan kwaikwayo na kasar Sin da ma'aikatan da suka gina filaye da dakunan wasannin Olimpic na birnin Beijing da tsofaffin mazaunan wurin wadanda aka sake musu matsuguni da sauran nagartattun ma'aikata na sana'o'I daban daban sun je kallon wasannin bisa matsayin rukunin farko. A wurin nuna wasannin dai kowa yana cike da halin fara'a, kuma dukan mutane suna ta yin tafi raf raf . Wani dan kallo mai suna Liu Xu shi ne daya daga cikin ma'aikatan gina dandalin nan, ya gaya wa manema labaru cewa, ga ni na shiga aikin gina dandalin nan tun daga ranar soma aikin ginawarsa, da idonmu muka ga yadda aka gina shi ta hanyar yin amfani da tubali da sauran kayayyakin gine-gine, ana iya cewa, mu muka gina dandalin nan tare da zubar da jini da gumi, yau da na je kallon wasannin bisa matsayin rukunin farko na 'yan kallo, na ji alfahari sosai da sosai.

'Yar kallo mai suna Liu Junmin ita ce mazauniya da aka sake mata matsuguni , Ta bayyana cewa, yau, na ji cewa, dole ne na je kallon wasannin a wurin, babban dalilin da ya sa haka shi ne saboda mun taba zama a wurin cikin shekaru fiye da 20, kuma muna kaunar wurin da muka taba zama. A gaskiya dai ba abu mai muhimmanci ba ne da dole ne mu je kallon wasannin, sai dai muhimmin abu shi ne don zuwa kallon ginin nan, dazun nan da muka sauka wurin, muna tafiya a kewayen dandalin, mun ji bambancin wurin da na da sosai, a gaskiya dai ya iya wakiltar gine-ginen hedkwatar kasar Sin.

Za a nuna wasanni har da sau 23, ciki har da wasannin kwaikwayo da aka nuna ta hanyar wake-wake da kide-kide da wasan ballet da dai sauran wasannin kwaikwayo na gargajiya don nuna godiya ga wadanda suka shiga ayyukan gina dandalin da mutane na rukunoni daban daban na zamantakewar al'umma. Sa'anan kuma domin yin gwaje-gwajen aiki da tsarin dandalin nan, da kuma yin share fage ga soma aiki da dandalin nan yadda ya kamata a yau da kullum.

1 2