Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-21 16:55:57    
Jin dadin zaman rayuwa yana da nasaba da kyakkyawan tabi'u

cri

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Jamus suka bayar, an ce, a cikin mutanen da suke jin dadin zaman rayuwarsu, mutanen da yawansu ya kai kashi 64 cikin dari suna son zama tare da abokan zama wato miji ko mata da abokai da kuma iyalai, kuma mutanen da yawansu ya kai kashi 50 cikin dari suna ganin cewa, su kan jin dadin zaman rayuwa yayin da suke a rana da kuma yin sumbatar masoya. Amma mutane masu yawa da ba su jin dadin zaman rayuwa su kan kashe dogon lokaci wajen wasannin na'urar kwamfuta, kuma kashi 69 bisa dari daga cikinsu sun nuna matukar sha'awa wajen kallon shafin Internet, yayin da kashi 45 bisa dari daga cikinsu suke son kallon talebijin.

Wata kwararriyar kasar Jamus a fannin nazarin hankalin mutane ta yi nazari cikin dogon lokaci kan dalilan da ya sa mutane suke jin dadin zaman rayuwa, kuma ta amince da sakamakon bincike da muka amtaba a baya. Bugu da kari kuma ta ba da shawarar cewa, mutanen da ba su jin dadin zaman rayuwa suna iya kara inganta jin dadin zaman rayuwarsu ta hanyar daidaita hankulansu.

Ban da wannan kuma wannan kwararriya ta bayyana cewa, ya kamata mutane su ba da taimako kullum ga wadanda suke bukatar taimako, da kuma nuna godiya da halin karamci ga wadanda suka taimake mu, kada a yi fatan samun zaman jin dadi daga sauran mutane. Idan kana so sauran mutane su gayyace ka, to dole ne ka gayyace su da farko.

Haka kuma ta bayyana cewa, jikin mutane zai samar da wani sanadari bayan sun yi wasannin motsa jiki, ta haka za su ji dadin zaman rayuwa. Ban da wannan kuma yayin da ake jin bakin ciki, wata kwalba ta kyakkyawan turare za ta iya faranta rai, sabo da kamshi wata kyakkyawar hanya ce wajen faranta zuciya. (Kande Gao)


1 2