Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-21 16:55:57    
Jin dadin zaman rayuwa yana da nasaba da kyakkyawan tabi'u

cri

A ran 15 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, kafofin watsa labarai na kasar Birtaniya sun bayar da labarin, cewa hukumar yin bincike kan kasuwanni da ke karkarshin jagorancin gwamnatin kasar ta gudanar da wani karamin bincike ga mazauna yara da matasa da masu matsakaitan shekaru da haihuwa da kuma tsoffi fiye da 1600 kan yadda suke jin dadin zaman rayuwarsu.

Daga baya kuma rahoton binciken ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne sabo da mazan da shekarunsu ya kai 35 zuwa 40 da haihuwa suke damuwa da wucewar lokacin kuruciya, ko kuma suna samun matsin lamba sosai daga wajen aiki da zaman rayuwa, shi ya sa suka fi nuna rashin jin dadin zaman rayuwa. A cikin wata takardar tambayoyi da aka maida maki 10 a matsayin makin koli, matsakaicin makin da wadannan maza suka samu ya kai 6.8, wanda shi ne maki mafi kankanta a cikin dukkan mutanen da aka gudanar da binciken gare su.

Ban da wannan kuma binciken ya bayyana cewa, yawancin maza suna ganin cewa, lokacin da shekarunsu ya kai 16 zuwa 24 da haihuwa, sun fi jin dadin zaman rayuwa, kuma matsakaicin makin da suka samu ya kai 7.55. Daga baya kuma makin ya samu raguwa bisa karuwar shekarunsu da haihuwa, amma makin ya sake samun karuwa bayan da suka yi ritaya, wanda matsakaicinsa ya kai kusan 7.8.

Game da mata na kasar Birtaniya, lokacin da shekarunsu ya kai 25 zuwa 34 da haihuwa, sun fi shan wahaloli a cikin zaman rayuwarsu. Rahoto ya yi bayanin cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kullum mata su kan shan aiki sosai wajen kula da yaransu a wancan lokaci. Daga baya kuma makin da suka samu wajen jin dadin zaman rayuwa ya samu karuwa sannu a hankali, ya zuwa shekarunsu ya kai 65 da haihuwa, wato bayan da suka yi ritaya, wannan maki ya kai matsayin koli wato 7.65.

Ban da wannan kuma manazarta sun gano cewa, zaman jin dadi ya sha bamban ainun tsakanin maza da mata masu aiki da marasa aiki, wato ke nan mata su kan fi maza jin dadin zaman alheri muddin dukkansu ba sa aiki.

Bisa sakamakon binciken da kasar Jamus ta bayar a 'yan kwanakin da suka gabata, an ce, jin dadin zaman rayuwa wani abu ne da na yau da kullum, kuma yana da nasaba da kyakkyawan tabi'u.

1 2