A shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Yuelianghu, ban da jin dadin kallon kyan karkara irin na garuruwan da aka fi samu ruwa a cikin kwale-kwale, masu yawon shakatawa kan fahimci kyan ganin hamada a kan rukuma. Shi ne babbar sigar musamman ta aikin yawon shakatawa a wurin. Yankin Alashan ya shahara ne a matsayin garin rakuma, inda rakuma masu kyan siffar jiki da kuma karfi suka yi zaman jituwa tare da mutane. Malam Sunbuer, wanda ke kiwon rakuma a shiyyar, ya bayyana ra'ayinsa kan aikinsa. Ya ce, 'Nisan da ke tsakanin gidana da tabkin Yuelianghu ya kai misalin kilomita 60. Iyalina kan zo tabkin tare da rakuma domin yin aiki a watan Mayu zuwa na Oktoba na ko wace shekara. Mu kan ci gaba da zamanmu a wurin makiyaya a sauran lokaci. A farkon lokacin da muke aiki a tabkin, muna da rakuma 5 zuwa 6. Amma yanzu saboda goyon baya da muka samu daga hukumar shiyyar, yawan rakumanmu ya karu fiye da 30. A shekarar bana, dimbin mutane sun kawo wa shiyyarmu ziyara, ko da yake ba mu da rakuma da yawa, amma mun sami kudin shiga da yawa, mun kuma kyautata zamanmu.'
A shekarar 2001, an soma bunkasa shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Yuelianghu bisa matsayinta na wurin yawon shakatawa da ke bayyana tsarin halittu masu rai irin na hamada. Manufa mafi muhimmanci da ake bi wajen raya shiyyar ita ce yin iyakacin kokari domin kiyaye dukkan abubuwan da suke kasancewa a asalin wuraren da suke a da. Malam Song Jun, shugaban kamfanin raya shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Yuelianghu, ya ce, 'A zahiri, nufinmu na raya tabkin Yuelianghu shi ne samar da wani misali na bunkasa aikin yawon shakatawa da ke nuna tsarin halittu masu rai. Muna neman shigo da masu yawon shakatawa a cikin wannan aiki, ta haka za su zama wanda ke san muhalin halittu masu rai da kara fahimtarsu a kai da nuna goyon baya da kuma shiga aikin kiyaye muhallin halittu a maimakon wanda ke ziyara kawai.'
A shekarun baya, masu yawon shakatawa baki sun yi ta kawo wa wannan kyakkyawan tabki ziyara.Masu sauraro, tare da wannan waka mai suna daren da wata ya bullo, makiyaya mazaunan tabkin Yuelianghu na jiran ku domin ziyarar garinsu. 1 2
|