Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-20 16:53:17    
Kai ziyara ga kyakkyawan tabkin Yuelianghu mai ban mamaki

cri

A jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta da ke arewacin kasar Sin, akwai wani yanki mai suna Alashan, inda akwai wani kyakkyawan tabki mai ban mamaki, sunansa shi ne Tenggelidalai Yuelianghu. Yau ma bari mu kawo masa ziyara tare.

A bakin 'yan kabilar Mongolia, ma'anar 'Tenggeli' ita ce sararin sama, ma'anar 'Dalai' kuwa ita ce tabki. Shi ya sa ma'anar cikakken sunan wannan tabki ita ce kyakkyawan tabki, wanda ke raka tekun da ke sararin sama. Saboda siffarsa ta yi kama da watar da ta karkace, shi ya sa mazaunan wurin kan kira shi takin Yuelianghu, wato tabkin wata.

Saboda gundumar Alashan ta hagu inda tabkin Yuelianghu yake tana fama da iska da rairayi, haka kuma, a kan yi fari da karancin ruwan sama, sa'an nan kuma, ana rana sosai, shi ya sa dimbin ruwa su kan bi iska. Hamadar Tenggeli hamada ce ta hudu a kasar Sin saboda girmanta, ita ce kuma hamada mafi saurin tashin rairayi sama domin bin iska. A cikin irin wannan hali ne kasancewar tabkin Yuelianghu ta fi nuna daraja.Wannan tsohon da ke rera mana waka shi ne Butugeqi. Bayan da ya yi ritaya daga aikinsa na malamin koyarwa, ya zo shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Yuelianghu domin yin aiki. A duk lokacin da masu yawon shakatawa sun zo wajen, da zarar suka sauka daga mota, sai Butugeqi da sauran makiyaya sun rera waka mai sigar musamman ta kabilar Mongolia, sun kuma bai wa baki farin kyallen da aka kira Hada da kuma giya mai dadin sha domin maraba da bakinsu daga wurare masu nisa.

A shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Yuelianghu, tsire-tsire masu tsayi sosai a kewayen tabkin, agwagi na iyo a kan ruwan. Ketare gadar katako da kuma ratsa tsire-tsire masu tsayi kan sanya masu yawon shakatawa su yi kuskure, wato suna ziyara a garuruwan da ke kudu da kogin Yangtse na kasar Sin, inda aka fi samun ruwa, a maimakon cikin hamada. Amma duk da haka, a lokacin da tuddan rairayi suka bullo a idanunsu, to, mutane na iya ganin kyan karkara irin na tabkin Yuelianghu.

Kyan karkara na tabkin Yuelianghu kan burge yawan masu yawon shakatawa da ke ziyara a wajen, bi da bi ne suke nuna matukar yabo. Malam Wang Ming da ya zo daga arewa maso yammacin kasar Sin ya ce, 'Lalle mun ji sakin jiki da farin ciki sosai a ko wane karo da muka kawo ziyara a nan. Kullum mu kan fuskanci babbar matsin lamba ta fuskar aiki, a karshen mako, mun zo nan mu kan kwana da dare, kashegari mun koma gida. Wannan ya ba da taimako a fannonin ci gaba da aiki da kuma sakin jiki.'

1 2