
Ban da wannan filim kuma, an riga an dauki filim fiye da 70 a wurin. Shi ya sa ana iya ganin gundumar gargajiya da dakunan shan shayi da na cin abinci da kantuna na lokacin da, haka kuma an iya ganin manyan dakunan kwana na mutane masu hannu da shuni, da dakunan kiwon dawaki da tumaki da dai sauransu.

Kamar yadda wani sanannen marubuci na kasar Sin Zhang Xianliang ya ce, idan babu basira da fasaha, wurin ba shi da daraja ko kadan.
Yanzu wurin daukar filim na Zhenbeipu ya riga ya zama wani muhimmin wurin shan iska na jihar Ningxia, kuma ya kawo wa jihar alheri sosai. 1 2
|