Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-19 21:33:07    
Wurin daukar filim na Zhenbeipu

cri

Yau na je wani wurin daukar filim da ake kiransa "Zhenbeipu" don yin ziyara. Har kullum ba na son wurin shakatawa da mutane suke gina da kansu, amma na ji mamaki sosai da na shiga wurin.

A lokacin da, wannan wurin wani muhimmin sansanin soja ne a daulolin Ming da Qing, wadda aka gina shi tare da loess wato kasa mai launin rawaya a kan makekiyar hamada. Amma wadannan gidajen tarihi sun jawo hankalin Zhang Yimou, wani shahararren derakta mai daukar filim na kasar Sin, inda ya yi wasu kayayyaki na wasan kwaikwayo. Filim mai suna "karo mai launin ja" da Mr. Zhang ya dauka a wurin ya samu lambar yabo na "Golden Bear" na karo na 38 a gun bikin filim na kasa da kasa da aka yi a birnin West Berlin, ta haka wurin daukar filim na "Zhenbeipu" ya shahara a duk fadin kasar Sin.

Muddin ka kalli filim "karo mai launin ja", sai ka iya samun dimbin abubuwa da ke cikin filim a wurin, kamar dakin samar da giya, da wurin kwana na 'yar wasan kwaikwayo da dai sauransu.

Wani mai ja-gorarmu ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa Mr. Zhang ya zabi wannan wuri shi ne sabo da kyan karkara da mutane da kuma al'adun gargajiya suna iya bayyana halin musamman na yankunan da ke arewa maso yammacin kasar Sin.

1 2