Ko da ya ke Yang Mei budurwa ce mai shekaru 28 da haihuwa ba ta yi aure ba tukuna,ta sha fadi da tashin zaman rayuwa a matsayin mata mai kula da yaran.Kan son zuciya da saukin fushin da yaran suka nuna,Yang Mei ta kan lallashe su da su gyara kuskurensu kamar yadda iyayensu suka yi musu.Abin da ya fi burge ta shi ne wani yaro karami da ake kiransa Haiwa a gidan yaran.Shi yaro ne mai kyakkyawa kuma mai wayo.Yayin da yake da shekaru takwas da haihuwa kawai,wani rikicin ya wakana tsakanin iyayensa,ubansa ya yi kuskure ya kashe uwarsa,an hukunta ubansa da aka tura shi gidan wakafi.Wannan al'amari ya girgiza Haiwa.Daga nan yaro mai kuzari ya zama yaro mai saukin fushi kuma ya sha bamban da sauran yara."Bayan da wannan al'amari ya faru,na ki jinin ubana.A ganina ubana ne ya rushe iyalina.Ka ga sauran yaran sun sami kauna daga iyayensu,amma ni babu.Na nuna hassada ga sauran yaran,na kaskanta ni kaina."
Kan wadannan yaran da zukatansu ya ji rauni,matan da ke kula da gidan yaran sun nuna musu kauna sosai sun warkar da raunin da suka ji a zukatansu kamar yadda uwayensu suka yi.Sun wanke fuskokinsu da kafafunsu,kuma sun raka su shiga barci da yi musu tatsuniyoyi masu ban sha'awa.Idan wani yaro yana fama da rashin lafiya,matan dake kula da gidan yaran su kan kasa hakuri su kan raka yaron dare da rana.Matan nan da ke kula da gidan sun nuna cikakkiyar kauna ga yaran da ke cikin wannan gida,amma sun rasa damar nuna kauna ga 'ya'yansu da namijinsu.
Ga shi a yau yaran dake cikin gidan nan suna girma cikin koshin lafiya tare da farin ciki bisa kulawar matan dake kula da gidan.Daga wannan gida na musamman,yaran sun gane mene ne aminci.sun riga sun koyi nuna tausayi ga saura.Bisa jagorar da matan kula da gidan suka yi musu,tunanin yaran ya fara canza su samu sabon ra'ayi kan mummunan al'amaran da suka ganewa idanunsu a da,haka kuma sun koyi fuskantar iyayensu yadda ya kamata,sun fara nuna kauna da ba da karfin gwiwa ga iyayensu da ake tsare a gidan wakafi,amma a da ba haka ba ne suka kin jinin iyayensu ne kawai.
Abin faranta rai ne ga matan dake kula da gidan yara yayin da tunanin yaran ya canza.Wani abu da ya fi sanya farin ciki shi ne wannan gidan kanana yara ya fara daukar hankulan zamantakewar al'umma.gwamnatoci da hukumomin ba da agaji da mutane da dama na wurin sun fara bayar da taimakon kudi da kayayyaki ga wannan iyali na musamman.Ko da ya ke zaman gidan kanana yara bai kai na masu arziki ba,amma mallama Pandu ta gamsu sabo da zaman yaran dake cikin wannan gidan ya samu karin kyautatuwa sosai.
Jama'a masu sauraro,kun dai saurari wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya rubuto mana kan wani gidan kanana yaran da iyayensu ke cikin gidan wakafi da wata macen da ta kafa wannan gidan yara.To,wannan ya kawo karshen bayaninmu na yau na "zaman rayuwar Sinna.Muna fatan kuna ci gaba da sauraronmu.(Ali) 1 2
|