Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-19 20:53:04    
Pan Du da gidanta na kanana yara

cri

Jama'a masu sauraro assalamu alaikum,barkanku da war haka.barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin "zaman rayuwa ta kasar Sin".A cikin shirinmu na yau za mu karanta wani bayani kan wani gidan kanana yara da ke bakin teku a yankin Lushun na birnin Dalian na arewa maso gabashin kasar Sin.Mallama Pan Du ta kafa wannan gidan yara ne musamman domin kula da yaran da iyayensu ke cikin gidan wakafi.

A cikin wani gini mai benaye biyu dake cikin kauyen Shuangdaigou na yankin Lushun,wakilin gidan rediyonmu ya gana da malama Pan Du wadda ake kiranta Mama mai nuna kauna a gidan kanana yara dake bakin teku.kafin shekaru hudu mallama Pan Du mai shekaru 38 da haihuwa ta yi kallon wata sinima inda aka nuna yadda wani dan sa kai ya taimaki wani matashin da ya aikata laifi a Hongkong na kasar Sin,tana so ta san ko akwai matasa kamar shi a wurin da take zama,sai ta ziyarci wasu gidajen wakafi a lardin Liaoning,mallama Pan Du ta girgiza saboda wani labarin da shugaban gidan wakafi ya gaya mata,ta ce "wata rana an tsugunar da wani namiji da matarsa a gidan wakafi sabo da sun aikata laifin sace kayayyaki daga wurin da ake gina manyan dakuna,kashegari an gano yaransu biyu namiji da mace sun durkusa a gaban kofar gidansu.Yaya za a yi,sai sashen ilmi ya dau nauyin kula da wadannan yara biyu."

A ganin mallama Pan Du ya kamata wadannan yara su more zaman jin dadi kamar yara na sauran iyalai.suna bukatar wani gida mai cike da kauna.Daga baya wata dabara ta fado mata.ta kafa wani gidan kananan yara da iyayensu ke gidan wakafi.

A yanayin kaka na shekara ta 2003,Pan Du ta yi murabus da aikinta,ta hada kanta da sauran abokanta masu arziki biyu da tattara kudin Sin Renminbi Yuan dubu hamsin,ta yi hayar gini mai benaye biyu a kauyen Shuanggou na yankin Lushun dake a birnin Dalian da kafa gidan kanana yara.Ta je gidajen wakafi na dab da birnin Dalian,ta kulla yarjejeniyoyin mika iznin kula da yara da iyayen yaran da suke zama a gidajen wakafi.Gidan kanana yara ya dau nauyin samar da kudi domin zaman yara da ilimintar da su.

Yawancin yaran dake cikin gidan sun taba yin zaman bariki sabo da ba su iya samun kauna daga iyayensu yadda ya kamata ba,idan an kwatanta su da yara na sauran iyalai suna da aibobi da yawa na rashin da'a.Yang Mei wata mata ce da ke kulawa da yaran ta gaya wa wakilinmu cewa ba aiki mai sauki ba ne na yin hulda da wadannan yara. Ta ce "da isowarsu a gidan,yaran su kan sa ido kan bako da nuna shakku.Idan ka taba wani kaya nasa,sai ya yi bakin ciki ko ya ce kada ka taba wannan abu,wannan abu nawa ne.wannan son zuciya ne da suka nuna.

1 2