
A cikin dakin nuna kayayyakin tarihi na daular Xixia, ana iya ganin wasu kayayyakin tarihi da aka samu daga kusheyin sarakunan daular. A ciki, wani shanun da aka yi da tagulla da zinari ya fi daraja, wanda ya iya shaidar fasahar yin amfani da zinariya. Ban da wannan kuma, akwai wani kayan tarihi da ake kiransa "tsuntsu mai dadin murya", shi wani abu ne na addinin Buddihsm, amma ba a taba ganin irinsa a sauran wurare ba.
Lokacin da muka fito daga dakin nuna kayayyakin tarihi, rana ta fadi, kusheyin sarakunan daular Xixia wadanda a kan kiransu "dala" da ke gabashin duniya sun yi kamar kananan duwatsu, suna watse a gindin dutsen Helan.

Watakila wasu mutane suna ganin cewa, kusheyin sarakunan daular Xixia ba wani kyakkyawan wurin shan iska ba ne, su wasu kananan duwatsu ne kawai. Amma kamar yadda a kan ce, wasu kyan karkara suna kan hanya, wasu kuwa suna cikin zuciya.(Kande) 1 2
|