
Yau, mun je kusheyin sarakunan daular Xixia da ke birnin Yinchuan domin yin ziyara da kuma fahimtar tarihin daular.
Daga shekara ta 1038 zuwa shekara ta 1227, an kasance da wata daular da wata karamar kabila ta kasar Sin ta kafa a arewa maso yammacin kasar Sin, wato daular Xixia. Birnin Yinchuan na yanzu, wato hedkwatar jihar Ningxia shi ne babban birnin daular. Kabilar Dangxiang, wani sashe na tsohuwar kabilar Qiang ita ce ta kafa daular, kuma bayan kafuwarta, ta samu bunkasuwa cikin matukar sauri, musamman ma sha'anin sake-sake. A cikin littafin "Marco Polo's travelogue", an bayyana cewa, kayayyakin da aka yi tare da gashin rakumai su kayayyaki ne mafi kyau a duk duniya. Shi ya sa an sayar da su zuwa wurare daban daban na kasar Sin da kuma kasashen duniya. Ban da wannan kuma fasahar sarafa karfe ta daular Xixia ta kasance cikin salum gaza a lokacan zamani, takubbanta sun shahara a duk kasar Sin.
Amma abin bakin ciki shi ne, a shekara ta 1227, sojojin daular Yuan da kabilar Mongolia ta kafa wadda ta fi karfi sun kai farmaki ga daular Xixia, wanda ya haddasa lallacewar daular. Haka kuma sabo da an kone ko da wawashen littattafai da kayayyakin tarihi na daular Xixia, shi ya sa daular ta zama tamkar wata daula ce da ba a iya fahimtarta ba.
1 2
|