Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-16 18:39:58    
Bunkasuwar tufafin musulmi a jihar Ningxia

cri

Shugaban masana'antar yin tufafin musulmi na Wantini Yang Jinxiang ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa aka kira wannan masana'anta da sunan 'Wantini' shi ne sabo da wannan kalma ta zo daga Larabci, kuma ma'anarta ita ce samar da taimako ga sauran mutane. Shi ya sa har kullum masana'antar tana bin ka'idar tsayawa tsayin daka kan adalci, da samun bunkasuwar tattalin arziki, da raya ayyuka bisa bukatun mutane, da kuma gina zamantakewar al'umma mai jituwa.

A da, a kan yi tufafi da hannu, shi ya sa ba a iya samun tufafi da yawa a ko wace rana ba. Domin kara saurin samar da tufafi, masana'antar Wantini ta sayo na'urorin zamani 4 a shekara ta 2005, wadanda darajar ko wanensu ta kai kudin Sin wato Yuan kimanin dubu 15 . Ta haka, yawan tufafin musulmi da masana'antar take samarwa ya ninka sau da yawa.


1 2 3