
Yau na je wata masana'antar samar da tufafin musulmi wadda ake kiranta "Wantini" da ke birnin Wuzhong da ke tsakiyar jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin don yin intabiyu. Jihar Ningxia wata jiha ce da ake iya samun musulmai mafi yawa a duk fadin kasar Sin, shi ya sa kayayyakin musulmi suna samun bunkasuwa kwarai da gaske a jihar.
An kafa wannan masana'antar samar da tufafin musulmi na Wantini a shekara ta 1998 bisa goyon bayan gwamnatin birnin Wuzhong. Kuma a lokacin kaka na shekara ta 2005, gwamnatin birnin ta tsai da kudurin kara karfin goyon bayan bunkasuwar masana'antar, wato ta samar da wani sabon wuri babba ba tare da karbar kudade a yanzu ba, sai dai bayan ta iya gudanar da ayyukanta kamar yadda ya kamata.
1 2 3
|