Bisa labarin da wani kamfanin dillancin labarai na kasar Japan ya bayar, an ce, manazarta masu ilmin kiwon lafiyar jama'a na jami'ar Tohoku ta kasar Japan sun gudanar da wani bincike tun shekara ta 1994 ga mutane fiye da dubu 40 da shekarunsu ya kai daga 40 zuwa 79 da haihuwa. Kuma manazarta sun kasa su cikin rukunoni hudu bisa yawan koren shayi da su kan sha.
Daga baya kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da wadanda su kan sha koren shayi yadda ya kamata, idan yawan karuwar koren shayi da suka sha, za su samu raguwar hadarin mutuwa sakamakon cututtukan kwakwalwa da zuciya. Yawan mutuwar maza da su kan sha koren shayi na kofuna biyar a ko wace rana zai iya raguwa da kashi 22 cikin dari idan an kwatanta su da wadanda ba safai su kan sha koren shayi har kofi guda a ko wace rana ba. Haka kuma game da mata, irin wannan hadari zai ragu da kshi 31 cikin dari. A cikin hadarin mutuwar mutane sakamakon toshewar jijiyoyin jini na kwakwalwa ya samu raguwa a bayyane, wato zai ragu da kashi 42 cikin dari ga maza sa'an nan zai ragu da kashi 62 cikin dari ga mata.
Bisa labarin da kamfanin watsa labarai na kasar Birtaniya ya bayar, an ce, masu ilmin kimiyya na jami'ar London ta kasar sun gano cewa, shan shayi zai iya ba da taimako wajen rage yawan sinadarin hormone mai kawo damuwar tunani da ke cikin jikin mutum, shi ya sa mutanen da su kan sha shayi sun fi saukin rage damuwar tunani idan an kwatanta su da wadanda su kan sha lemo.
Manazarta sun kasa samari maza 75 da su kan sha shayi cikin rukunoni biyu, da kuma gudanar da wani bincike na tsawon makwanni shida gare su. Domin magance kuskuren sakamakon binciken sakamakon tasirin da launi da kamshin shayi su kan bai wa masu shiga binciken, manazarta sun yi amfani da abin sha da ke da launin shayi a maimakon shayi na gaskiya. Mutanen da ke cikin rukuni daya sun sha irin wannan abin sha da ke kunshe da sinadarin da ke cikin shayi, amma mutanen da ke cikin dayan rukunin sun sha irin wannan abin sha da ke da kamshin shayi amma ba tare da sinadarin da ke cikin shayi ba.
Lokacin da ake gudanar da wannan bincike, wandannan mutane 75 sun samu damuwar tunani iri daban daban, kamar barazanar rashin samun aikin yi, da karar da aka kai su kan tuhumar satar kayayyaki a cikin kantuna da dai sauransu.
A waje daya kuma manazarta sun nazarci yawan sinadarin hormone mai kawo damuwar tunani da ke cikin jikin mutum, kuma sakamako ya bayyana cewa, bayan mintoci 50 da mutanen da suka sha abin sha da ke kunshe da sinadarin da ke cikin shayi, yawan irin wannan sinadarin da ke jikinsu ya ragu da kashi 47 bisa dari, haka kuma yawan irin wannan sinadarin da ke cikin jikin mutanen da suka sha abinsha iri daba ya ragu da kashi 27 bisa dari kawai.(Kande Gao) 1 2
|