Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-14 15:17:18    
Shan shayi yadda ya kamata zai ba da taimako wajen lafiyar jikin dan Adam

cri

Bayan da masu ilmin kimiyya na kasashen Birtaniya da Amurak suka gudanar da wani bincike, sun gano cewa, wani sinadarin da ke cikin koren shayi wato green tea zai iya hana kwayoyin cutar kanjamau su kasance a kan kwayoyi masu kare garkuwar jiki.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Birtaniya suka bayar, an ce, manazarta sun gano cewa, koren shayi yana kunshe da wani sinadari mai suna EGCG, idan irin wannan sinadari ya kasance a kan kwayoyi masu kare garkuwar jiki da farko, to kwayoyin cutar kanjamau ba su da damar kasancewa a kansu.

Furofesa Williamson na jami'ar Sheffield ta kasar Birtaniya ya ce, sakamakon nazarin da muka yi ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne shan koren shayi zai ba da taimako wajen rage hadarin kamuwa da cutar kanjamau da kuma rage yaduwar kwayoyin cutar.

Amma a waje daya kuma ya jaddada cewa, shan koren shayi ba zai iya warkar da cutar kanjamau ba, haka kuma ba zai iya shawo kan cutar ba. Amma game da mutanen da suke fama da cutar kanjamau, shan koren shayi zai iya sassauta halin da suke ciki dangane da cuta.

Ba kawai shan koren shayi zai iya ba da taimako wajen sassauta cutar kanjamau ba, har ma zai iya rage hadarin mutuwar mutane sakamakon toshewar jijiyoyin jini na kwakwalwa.


1 2