Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-14 15:11:52    
'Yan wasan Sin matasa sun jawo hankulan mutane a gun taron wasanni na birane na kasar Sin a karo na 6

cri

In an yi tambayar su wane ne suka fi ba mutane ban mamaki a wannan karo, to, amsa ita ce 'yan wasan ninkaya 2 wato Li Xuanxu mai shekaru 13 da haihuwa da kuma Li Zhesi mai shekaru 12 da haihuwa. Li Xuanxu ta sami lambobin zinariya a cikin gasar ninkaya mai salo daban daban mai tsawon mita 200 da 400 da kuma gasar ninkaya cikin 'yancin kai na tsawon mita 800, haka kuma, ta sami maki mafi kyau a gare ta a cikin gasannin, ta kai matsayin farko na shiga taron wasannin Olympic. Babu tantama tana da karfin shiga taron wasannin Olympic na Beijing.

Li Zhesi, wadda ta soma koyon ninkaya a lokacin da shekarunta ya kai 6 da haihuwa kawai, ta sami lambobin zinariya 2 a yini daya, ta haka, ta zama zakara mafi kankanta a cikin gasannin ninkaya a gun taron wasanni na birane na kasar a wannan karo. Li Zhesi ta gaya mana cewa, a farkon gasannin, ta yi iyakacin kokarinta. Ta ce,'Ko shakka babu na ji matukar farin ciki saboda na zama ta farko. Na rubanya kokarina a hanya mai tsawon mita 50.'

In an kwatanta Ma Long da Liao Yali, wadanda suka kaddamar da ayyukan share fagen taron wasannin Olympic na Beijing ba da jimawa ba, Li Xuanxu da Li Zhesi suna matakin aza harsashe. Taron wasanni na birane na kasar mafari ne a gare su domin cimma burinsu, suna fuskantar doguwar hanya, suna da dimbin buri domin cimmawa. Sa'an nan kuma, kasar Sin tana fuskantar kyakkyawar makoma a fannnin wasannin motsa jiki saboda wadannan 'yan wasa matasa.(Tasallah)


1 2 3