Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-14 15:11:52    
'Yan wasan Sin matasa sun jawo hankulan mutane a gun taron wasanni na birane na kasar Sin a karo na 6

cri
Ran 3 ga wata, a birnin Wuhan da ke kudancin kasar Sin, aka rufe taron wasannin motsa jiki na birane na kasar Sin a karo na 6. Taron wasanni na wannan karo gagarumin taron wasanni ne na karshe da kasar Sin ta kira kafin taron wasannin Olympic na Beijing, inda 'yan wasa fiye da 6300 daga kungiyoyin wakilai 74 suka halarta, shi ya sa dukkan yawan 'yan wasa da girman taron sun karya matsayin bajimta a tarihin wannan taron wasanni. Bisa ka'idojin da aka tsara, 'yan wasan da suka shiga taron wasanni na birane shekarunsu bai kai 20 da haihuwa ba, shi ya sa aka mayar da wannan taron wasanni tamkar dandamali ne ga matasa da su nuna gwanintarsu daga dukkan fannoni. A wannan shekara, dimbin 'yan wasa matasa sun sami maki mai kyau, sun faranta wa mutane rai da kuma ba su ban mamaki. Mai yiwuwa ne ba za su taka muhimmiyar rawa a gun taron wasannin Olympic a shekara mai zuwa ba, amma duk da haka, ko shakka babu suna matsayin kwararru na bayan fage ne da kasar Sin ke matukar bukata domin raya wasannin motsa jiki.

Wasan kwallon tebur wani irin wasa ne da kasar Sin ke mayar da shi a gaban sauran wasanni. 'Yan wasa Ma Long da Guo Yue da sauran mambobin kungiyoyin kasar sun shiga gasannin wasan kwallon tebur na taron wasanni na birane na kasar a karo na 6, a ciki kuma Ma Long ya zama zakara a cikin gasar ta tsakanin maza. A ra'ayinsa game da gasar, Ma Long ya ce, dukkan 'yan wasan da suka shiga taron wasanni na birane matasa ne, kuma malaman horas da wasanni na kungiyoyin kasar masu yawa sun je filin wasan domin dudduba da kuma jarraba wadannan matasa. Shi ya sa wannan taron wasanni na da matukar muhimmanci wajen ci gaban 'yan wasa matasa a nan gaba. Ba tare da boye kome ba wannan zakara mai shekaru 19 da haihuwa ya bayyana cewa,'A galibi dai, a lokacin da na zo muhimmin mataki, ban ta da hankali ba, ina da karfin zuciya sosai. Na yi fintikau a muhimman matakai, shi ya sa na sami nasara.'


1 2 3