Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-13 17:10:24    
Yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin na Yunnan na kasar Sin na bude kofa ga kasashen duniya

cri

Shigar da yankin Shilin wato yanki mai dimbin duwatsu cikin jerin kayayyakin tarihi na halitta na duniya ba kawai ba faranta ran kwararrun da abin ya shafa da kuma jami'an kula da harkokin wannan shiyya ba, har ma wadanda suka kawo wa shiyyar ziyara a karo na farko sun ji farin ciki bisa nasarar da yankin Shilin ya samu. Madam Sadi, 'yar kasar Australia amma asalinta kasar Sin ne, ta ce, 'A idona, yankin Shilin kyakkyawan wuri ne. A gaskiya mun ji alfahari sosai saboda ta sami nasarar zama kayan tarihi na duniya. In karin baki su kawo masa ziyara, to, za mu ilimantar da su al'adun kasar Sin yadda ya kamata.'

Yanzu akwai wuraren tarihi na duniya fiye da 830 a kasashe kusan 140. Malam Liang ya kara da cewa, ana bin tsauraran matakai a fannin zaben wuraren tarihi na halitta na duniya, in an kwatanta da zaben wurare ko kuma kayayyakin tarihi na al'adu na duniya. Dalili mafi muhimmanci da ya sa yankin Shilin na kasar Sin ya ci nasara shi ne domin ya tabbatar da sharudda 2. Ya ce, 'Da farko shi ne a fannin ilmin fasaha. Yankin Shilin, abun al'ajabi ne irin na halitta a duniya, wanda aka samu bisa ikon Allah. Na biyu kuma, darajar yankin Shilin a fannin kimiyya ita ce ya nuna tsarin yanayin kasa mai sigar musamman, wato Yankin Shilin ya bayyana tarihin canje-canjen duniyarmu ta hanyar tsarin yanyin kasa na Karst.'

A shekarar 1991, yankin Shilin ya gabatar da rokon zama wurin tarihi na halitta na duniya a karo na farko a matsayin shiyyar yawon shakatawa ta kasar Sin da ke nuna tsarin yanayin kasa na Karst, amma saboda wasu dalilai, yankin Shilin ya janyo rokonsa da kansa. Duk da haka, bayan wannan, a cikin shekaru kusan 17 da suka wuce, mazaunan yankin Shilin sun yi ta yin kokari domin shigar da garinsa cikin jerin wuraren tarihi na halitta na duniya ba tare da kasala ba. A karshe dai, sun ci nasara.

Malam Li Zhengping ya yi bayanin cewa, zama wurin tarihi na kasa da kasa wani sabon mafari ne ga yankin Shilin. Hukumarsa za ta tabbatar da zuba isassun kudade domin inganta hanyoyin da take bi a fannin kiyaye yankin Shilin ta fuskar kimiyya daga dukkan fannoni tare da mayar da tsara shiri bisa ilmin kimiyya tamkar sharadin farko, haka kuma, za ta yi kokari domin raya yankin Shilin zuwa yankin kiyaye wuraren tarihi na halitta na duniya da zai ba da misali ga takwarorinsa na sauran kasashen ketare.


1 2