Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-13 17:10:24    
Yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin na Yunnan na kasar Sin na bude kofa ga kasashen duniya

cri

Ran 27 ga watan Yuni a shekarar da muke ciki, a gun babban taron kayayyakin tarihi na kasa da kasa a karo na 31 da aka yi a birnin Christchurch na kasar New Zealand, bayan da aka dudduba da kuma kada kuri'a a kai, yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin ya zama wurin tarihi na halitta na duniya. Malam Liang Yongning, wani kwararre mai ilmin kayayyakin tarihi na duniya, wanda ya yi shekaru 30 yana nazarin yankin Shilin, ya bayyana cewa, shigar da yankin Shilin cikin jerin kayayyakin tarihi na halitta na duniya ya cimma burinsa mai tsawon yawan shekaru. Ya ce, 'A lokacin da na zo nan domin samun horo a matsayin wani dalibi a shekarar 1978, yankin Shilin ya burge ni sosai, amma a lokacin, ko kusa ban yi tsammani cewa, zan ci gaba da nazari kansa ba, ina sha'awar yankin Shilin kwarai. A duk shekara, na sha zuwa yankin Shilin, har ma wasu duwatsu sun yi kama da abokan azikina, na kan taba su a ko wane karo da na ga su. Wannan na da ban sha'awa ainun.'

A matsayin jami'in kula da harkokin shiyyar yawon shakatawa ta Shilin, malam Li Zhengping, shugaban hukumar kula da harkokin shiyyar yawon shakatawa ta Shilin, yana ganin cewa, mazaunan yankin Shilin da dimbin mutanen da ke mai da hankulansu kan wannan yanki, wadanda ba a iya kidaya yawansu ba, sun rubanya kokari da kuma zura ido kan ganin yankin Shilin ya sami nasarar zama wurin tarihi na duniya. Ya ce, 'Yankin Shilin ya sami nasarar zama kayan tarihi na halitta na duniya. Wannan na da muhimmanci sosai ba kawai ga yankin Shilin da Kunming ba, har ma ga kasar Sin, ya zama alama ta kasar Sin. A matsayin wani Basinne, in ana cewa, yankin Shilin da ya shahara a duniya a yanzu ya kawo wa kasar Sin girmamawa. A ganina, kamata ya yi ko wane Basinne ya ji alfahari domin yankin Shilin.'

1 2