Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-12 14:34:03    
An shimfida bututun gas da ke tsakanin jihar Shaanxi da birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin

cri

Da ya ke wuraren da aka shimfida bututun gas a tsakanin jihar Shaanxi da birnin Beijing wurare ne da duwatsu su kan gunguro da samun zaizayewar kasa da tabo, ana kula da batutun gas ta hanyar zamani don ba da tabbaci ga jigilar gas daga jihar Shaanxi zuwa birnin Beijing. Dokta Dong Shaohua, shugaban cibiyar kimiyya da fasaha ta kamfanin man fetur na kasar Sin a birnin Beijing ya bayyana cewa,

"mun harhada na'urori na zamani a tashoshin bututun gas, wadannan na'urori na samar da labaru zuwa ofishinmu da ke a birnin Beijing. Wato a birnin Beijing muna iya samun labaru a kan yadda ake gudanar da harkokin bututun gas. Idan wani abu ya sami aikin bututun gas, to, za mu shugabanci ma'aikata masu gyaran bututuwan da ke a wurin su gyara bututun daga birnin Beijijng, har zuwa lokacin da suka gama aikinsu na gyarawa."

A sakamakon samar da isasshen gas ga birnin Beijing, an canja tsarin makamashi na birnin Beijing. Yanzu, ba ma kawai mazaunan birnin suna amfani da gas da ba ya gurbata muhalli ba, har ma bos iri iri da yawansu ya wuce 4,000 su ma za su amfani da gas a birnin. Malam Liu Lei, babban manajan babban kamfanin man fetur da gas na Beijing na rukunin man fetur na kasar Sin ya jiku sosai cewa, "yanzu muna jigilar gas da yawansu ya wuce cubic mita biliyan 10 zuwa Beijing ta hanyar wadannan hanyoyin bututun gas biyu da ke tsakanin jihar Shaanxi da birnin Beijing. Ta haka muna ba da tabbaci ga samar da gas ga birnin Beijing, kuma za mu ba da tabbaci ga samar da gas a lokacin da ake shirya wasannin Olympic na Beijing a shekarar badi. Saboda haka za mu dauki matakai daban daban domin kammala aikinmu na samar da gas musamman yayin da za a shirya wasannin Olympic na Beijing. (Halilu)


1 2