A watan satumba na shekarar 1997, aka fara jigilar gas daga jihar Shaanxi a yammacin kasar Sin zuwa birnin Beijing, hedkwatar kasar, ta hanyar bututun gas wanda tsawonsa ya kai kimanin kilomita dubu daya. Wannan bututun gas yana da tsawo sosai, kuma an shimfida shi ne a tsakanin jihar Shaanxi da birnin Beijing. Ya zuwa yanzu, an yi shekaru 10 ana jigilar gas daga yammacin kasar Sin zuwa biranen Beijing da Tianjin.
A watan Mayu na shekarar 1996, aka fara aikin shimfida bututun gas a tsakanin jihar Shaanxi da birnin Beijing, wanda tsawonsa ya kai kilomita 910. Bututun shi ne na farko da aka shimfida a tsakanin jihar Shaanxi da birnin Beijing. A sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin birnin Beijing, a shekarar 2005, an kaddamar da irin bututun nan na biyu da ke jigilar gas daga jihar Shaanxi zuwa birnin Beijing, wanda tsawonsa ya kai kilomita 935. Yawan gas da aka yi jigilarsa daga jihar Shaanxi zuwa Beijing ta bututun nan biyu ya kai cubic mita biliyan 17.5 a cikin shekaru 10 da suka wuce, kuma ya dauki sama da kashi 95 cikin dari bisa na duk gas da aka yi amfani da su a duk birnin Beijing.
Ma'aikata masu gyaran wadannan bututun gas suna kokari sosai wajen ba da tabbaci ga jigilar gas daga jihar Shaanxi zuwa birnin Beijijng yadda ya kamata. Malam Wu Zhonglin, wani jami'in reshen masu gyaran bututun gas na kamfanin man fetur na kasar Sin a birnin Shuo na jihar Shaanxi ya yi takama da ma'aikatan aikinsa cewa, "batutun gas da muke kulawa suna shafar zaman rayuwar jama'a da harkokin tattalin arziki na biranen Beijing da Tianjin. Saboda haka wajibi ne, mu yi aikinmu da kyau sosai. Tun bayan da aka kaddamar da wadannan bututun gas a cikin shekaru da yawa da suka wuce, ba a gamu da hadari mai tsanani wajen aiki da batutun ba. Aikinmu ya tashi kamar daidai da na ma'aikata masu kashe wuta. Yanzu, idan wata matsala ta faru, to, za mu je wurin faruwar matsala nan da nan don daidaita ta cikin sauri. Na iya tabbatar da cewa, idan hadarin bututun gas ya auku a falalin fili da ba hawa da sauka, to, za mu kawar da shi cikin awa 20."
1 2
|