Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-09 16:04:31    
Kasar Sin ta yi hakikanan ayyuka domin ciyar da yunkurin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur gaba

cri

Na biyu, kasar Sin ta aika da reshen sojojin injiniya don shiga hadaddiyar rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da ke shiyyar Darfur ta M.D.D. da kungiyar tarayyar Afrika, wato AU.

Na uku, kasar Sin ta ba da taimakon jin kai ga shiyyar Darfur. Yanzu, kayayyaki da kudin ba da taimako na farkon matakai uku sun riga sun isa Darfur, kuma ana jigilar na hudu da na biyar daya bayan daya zuwa shiyyar.

Na hudu, kasar Sin na sa himma don shiga ayyukan raya shiyyar Darfur, da kuma sa kaimi ga warware matsalar Darfur. Yanzu, akwai wani kamfanin kasar Sin yana shiga ayyukan samar da ruwa a jihar Janub Darfur, don sassauta halin rashin ruwa da wurin ke ciki. Wani kamfanin kasar Sin daban kuma yana shirya tabbatar da aikin samar da ruwa a jihar Shimal Darfur. Bayan haka kuma, kamfannonin kasar Sin da ke Darfur suna yin amfani da ma'aikata da yawa daga Darfur, ta yadda halin zaman rayuwa da mutanen shiyyar ke ciki ya samu kyautattuwa sosai.

Kakakin kungiyar musamman ta AU ya nuna yabo sosai ga taimakon da kasar Sin ta bayar wajen warware matsalar shiyyar Darfur, yana ganin cewa, kasar Sin ita ce muhimmiyar abokiya ta AU kan batun Darfur.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau ke nan, Bilkisu ke cewa ku huta lafiya.(Bilkisu)


1 2