Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-09 16:04:31    
Kasar Sin ta yi hakikanan ayyuka domin ciyar da yunkurin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur gaba

cri

A ranar 23 ga watan Oktoba na bana, a lokacin da jirgin kasa na musamman da ke jigilar kayayyakin ba da taimako da kasar Sin ta bayar ga shiyyar Darfur ta kasar Sudan ya isa birnin Nyala, hedkwatar jihar Janub Darfur, gwamnatin kasar Sudan ta shirya gagarumin bikin nuna maraba da bayar da kayayyakin. Ministan makamashi da ma'adinai na kasar Sudan Awad Ahmed Al-Jaz ya yi jawabi a gun bikin cewa, "Gwamnatin kasar Sin ta nuna hali na hakika kan warware matsalar Darfur."

A lokacin da wannan jirgin kasa na musamman ya tashi daga birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan zuwa shiyyar da ke yammacin Darfur, gwamnatin Sudan ta kara shirya babban bikin ban kwana. Kafofin watsa labaru na kasar Sudan sun bayar da labari cewa, wadannan bukukuwa biyu sun nuna cewa, gwamnati da jama'ar Sudan suna mai da hankali da kuma nuna godiya ga hakikanan taimakon da kasar Sin ta bayar kan sa kaimi ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya a Darfur.

A lokacin da yake zantawa da manema labaru na kamfanin dillancin labaru na Xinhua, Mr. Li Chengwen, jakadan kasar Sin da ke kasar Sudan ya bayyana cewa, kokarin da kasar Sin ta yi wajen ba da taimako don warware matsalar shiyyar Darfur kamar yadda ya kamata, yana dacewa da manufofin taimakawa kasashen Afrika kan tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa. Muhimman fannoni guda hudu da kasar Sin ke yin kokari a kai su ne:

Da farko, kasar Sin na sa himma domin shiga da ciyar da yunkurin siyasa na Darfur. A lokacin da shugaba Omer Hassan Ahmed Elbashir na kasar Sudan ke yin ziyara a kasar Sin da kuma halartar taron koli a Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika a watan Nuwamba a shekarar da ta wuce, da kuma lokacin da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ke yin ziyara a Sudan a watan Febrairu na bana, shugabannin kasashen biyu sun yi shawarwari, inda suka yi musayar ra'ayoyinsu kan batun Darfur. Bugu da kari kuma, kasar Sin na shiga tattaunawar da ke da nasaba da batun Darfur da M.D.D. ta yi, kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen zartas da kuduri mai lamba 1769 game da batun Darfur da kwamitin sulhu ke yi. Kazalika kuma tun bayan da Mr. Liu Guijin ya hau kan kujerar wakilin musamman na gwamantin kasar Sin kan batun Darfur a watan Mayu na bana, ya riga ya kai ziyara har sau uku a shiyyar Darfur. Bayan haka kuma, ya halarci taro da shawarwari sau biyu da aka shirya a kasar Libya game da batun Darfur.

1 2