Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-07 17:56:21    
An kafa dandalin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen waje ta hanyar nunin baje kolin littattafan kasa da kasa a birnin Beijing

cri

Nunin baje kolin littattafan kasa da kasa na Beijing an soma shirya shi ne a shekarar 1986, girmansa ya kara habakawa, kuma ingancinsa ya kara samun kyautatuwa. Duk fadin filin nunin da aka samu a wannan gami ya kai murraba'in mita dubu 34, wanda ya karu da kashi 30 cikin dari bisa na shekarar da ta shige, ire-iren littattafan da aka yi nuninsu ya kai dubu 100 ko fiye, duk wadannan sun wuce na sauran nune-nunen da aka yi a tarihi.

Kasar Jamus babbar bakuwa ce a gun nunin baje kolin nan, ta tura madaba'arta da yawansu ya kai 42 tare da littattafai iri iri 1500 ko fiye, sa'anan kuma a wurin yin nunin baje kolin, kasar ta shriya makon Jamus na nuna littattafai. Ministan al'adu na kasar Jamus Bernd Neumann ya bayyana cewa, a ganinmu, bisa babbar kasa bakuwa a gun nunin, abin alfahari ne gare mu, muna fatan bayyana al'adunmu da adabinmu ta hanyar nunin ta yadda mutane kasar Sin sai kara yawa suke yi su iya kara fahimtar fannin nan namu.

A lokacin da aka shigo da littattafai daga kasashen waje na duniya, ana sa kaimi ga ayyukan madaba'a na kasar Sin wajen tinkarar zuwa duniya. A cikin jawabin da mataimakin shugaban koli na kamfanin Amazon .Com Mr Diego Piacentine ya yi, ya bayyana cewa, don biyan bukatun da dimbin masu karantawa suke yi na karanta bayanan da kasar Sin ta da'ba, tashar internet ta Amazon ta riga ta sami littattafan da aka rubuta da Sinanci da iren iren yawansu ya kai dubu 80 kuma ire-irensu da za a iya zabensu sai kara karuwa suke yi .

Kafin shekaru biyu da suka wuce, kasar Sin ta soma aiwatar da shirinta na sayar da littattafanta a kasashen waje. Ta hanyar samar da kudade a kyauta ne ta himmantar da kasashen waje wajen fassara littattafan da kasar Sin ta buga.

Sa'anan kuma, an bayar da lambar musamman ta samar da gudumuwa ga littattafan kasar Sin a lokacin nunin beje kolin , masanin harshen Sinanci na kasar Jamus da sauransu biyu sun sami lambar. Mr Kubin Wolfgang ya bayyana da harshen Sinanci cewa, kuna dogara bisa karfin masanan harshen Sinanci don yada abubuwanku, amma mu ne tsirarru, sa'anan kuma muna da ra'ayinmu na kanmu da bai dace da naku sosai ba. A kasar Sin da akwai mawallafai da masana mafi yawan gaske, mun iya karanta littattafansu kadan ne ba da yawa ba, saboda haka ya kamata ku horar da masana da mawallafai da masu aikin madaba'a da suke magana da harsunan waje da yawa don su mai da hankali ga bayyana mana nagartattun littattafanku da sauran abubuwa gare mu. (Halima)


1 2