Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-07 17:56:21    
An kafa dandalin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen waje ta hanyar nunin baje kolin littattafan kasa da kasa a birnin Beijing

cri

Kwanan baya, an yi bikin rufe nunin baje kolin littattafan kasa da kasa na shekarar 2007 a birnin Beijing tare da nasara , 'yan kasuwa na madaba'ar gida da na waje sun nuna himma da kwazo don halartar nunin, a ganin mutanen rukunonin littattafai na gida da na waje, nunin baje kolin littattafai na birnin Beijing ya riga ya zama wani dandali mai muhimmanci sosai na yin ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen waje.

Bisa matsayin nuni mafi girma da aka shirya a Asiya a halin yanzu, an bude nunin baje kolin littattafai na kasa da kasa na shekarar 2007 a birnin Beijing daga ranar 30 ga watan Augusta zuwa ranar 3 ga watan Satumba na shekarar da muke ciki, hukumomin madaba'a 1400 ko fiye da suka zo daga kasashe da jihohi 58 sun halarci nunin, wasu shahararrun hukumomin madaba'a na kasar Amurka da na Singapore da sauran kasashe su ma sun halarta bisa matsayinsu na 'yan kallo, kasar Bangaladesh da Amman da Afrika ta kudu da hadadiyyar daular Larabawa da Azerbaijan da Uzbekstan su 6 na Asiya da Afrika su ma sun hallarci nunin a karo na farko. A gun bikin budewar nunin, shugaban babbar hukumar kula da aikin watsa labaru da da'bi ta kasar Sin Mr Liu Binjie ya bayyana cewa, bisa matsayinsa na yin cudandar ayyukan da'bi na kasar Sin da na kasashe daban daban na duniya, kuma bisa matsayin sarari da dandali masu fadi sosai na yin ma'amala a tsakanin masu aikin madaba'a na gida da na waje, ana fatan mutanen rukunonin madaba'a na gida da na waje su yi amfani da damar shirya nunin sosai, don yin ayyukan ciniki da ikon mallakar buga littattafai da sauran irinsu da yin musanya ra'ayoyi a kan ayyukan da'bi, su yi koyi da juna, kuma gaba dayansu suke sa kaimi ga raya ayyukan da'bi a kasa da kasa.

1 2