Bisa ra'ayoyin shugabannin kasashen Sin da Rasha, an shirya bikin "Shekara domin kasar Rasha" a kasar Sin a shekarar 2006, kuma an shirya bikin "Shekara domin kasar Sin" a kasar Rasha a shekarar 2007 domin kara yin musanye-musanye da hadin guiwa a fannoni daban-daban a tsakanin kasashen biyu. A gun bikin rufe "Shekara domin kasar Sin" da aka shirya a kasar Rasha, Mr. Wen Jiabao da takwaransa na kasar Rasha Viktor Zubkov sun yaba wa sakamakon da aka samu a gun irin wannan bukukuwa.
Daddin dadawa kuma, Yang Jiechi ya ce, kasashen Uzbekistan da Turkmenistan da Bylerus sun kuma mai da hankulansu sosai kan ziyarar Wen Jiabao. Lokacin da Wen Jiabao ke yin ziyara a wadannan kasashe 3, kasar Sin da wadannan kasashe uku sun daddale jerin yarjejeniyoyin yin hadin guiwa. Lokacin da yake ganawa da yin shawarwari da shugabannin wadannan kasashe 3, Wen Jiabao ya ce, bangaren kasar Sin ya girmama wa hanyar neman cigaba da jama'ar kasashen uku suka zaba da kansu, kuma yana goyon baya ga kokarin da kasashen uku suke yi domin kiyaye ikon mulkin kasa da tabbatar da tsaron kai da kuma neman cigaban tattalin arzikinsu. 1 2
|