Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-07 17:55:00    
Tabbatar da abuta da kuma raya hakikiyar hadin guiwa tsakanin kasar Sin da kasashen da ke makwabtaka da ita

cri

A ran 7 ga wata da safe, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya dawo nan birnin Beijing bayan da ya kammala ziyararsa ta aiki a kasashen Asiya da na Turai 4. A kan hanyar dawowarsa a nan birnin Beijing, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi wanda ya raka Wen Jiabao ya gana da wakilan kafofin watsa labaru na kasar Sin, inda ya bayyana cewa, ziyarar da Wen Jiabao ya yi a wannan karo ta taka rawa sosai wajen tabbatar da huldar sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Uzbekistan da Turkmenistan da Bylerus da Rasha, da kuma amincewa da juna kan harkokin siyasa da hadin guiwar da ake yi a tsakaninsu bisa halin da ake ciki yanzu.

Tun daga ran 2 zuwa ran 6 ga wata, Wen Jiabao ya yi ziyarar aiki a kasashen Uzbekistan da Turkimenistan da Bylerus da Rasha, kuma ya halarci taro a karo na 6 na firayin ministocin kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai da taron ganawa a karo na 12 da aka saba shiryawa a tsakanin firayin ministocin kasashen Sin da Rasha da kuma bikin rufe "Shekara domin kasar Sin" da aka yi a kasar Rasha. Ko da yake Wen Jiabao ya yi ziyara a wadannan kasashe 6 cikin kwanaki 5 kawai, amma ya halarci bukukuwa iri iri.

A gun taron firayin ministocin kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai a karo na 6, Wen Jiabao ya gabatar da hakikanan matakai kan yadda za a karfafa da raya hadin guiwa a tsakaninsu. Yang Jiechi ya ce, jerin shawarce-shawarcen da Wen Jiabao ya gabatar sun ciyar da hadin guiwar da ake yi bisa halin da ake ciki a tsakanin kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai gaba. A waje daya, Mr. Yang ya sanar da cewa, shugabannin da suka halarci wannan taro sun kuma amince da ra'ayoyin da Wen Jiabao ya bayar.

Bugu da kari kuma, lokacin da Wen Jiabao yake ziyara a kasar Rasha, shi da shugabannin kasar Rasha sun sami ra'ayi daya kan yadda za a raya huldar abokantaka irin ta hadin guiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, kuma sun rattaba hannu kan jerin yarjejeniyoyi na yin hadin guiwa. Lokacin da yake ganawa da shugabannin kasar Rasha, Wen Jiabao ya jaddada cewa, bangaren kasar Sin zai kara aiwatar da tunanin tabbatar da zaman lafiya da neman ci gaban huldar siyasa da ta tattalin arziki a tsakanin Sin da Rasha bisa ka'idar "Sada zumunta har abada da neman cigaba cikin hadin guiwa" a tsakaninsa da kasar Rasha. Haka kuma, bangaren Rasha ya jaddada cewa, kasar Rasha za ta ci gaba da yin kokari wajen kara yin hadin guiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsa da kasar Sin. Kuma zai kara yin hadin guiwa mai dorewa cikin dogon lokaci mai zuwa a tsakaninsa da kasar Sin.

1 2