Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-06 14:59:10    
Fahimtar yanayin al'adun kabilu a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin a kasar Sin

cri

A shiyyar yawon shakatawa ta Shilin, a ranar da aka yi bikin mika wutar yola, mutane kan taru da sassafe. A tsakiyar rana, bayan da aka busa kaho, dimbin matasa maza da mata masu sanya kyawawan tufafi irin na kabilar Yi sun yi raye-raye tare da kida, sun shiga babban fili. Mutane masu matsakaicin shekaru kuwa sun yi wasa da sauran kayayyakin kida domin raka matasa. Jim kadan babban filin cike yake da matukar murna.

Yayin da dare ya yi duhu, 'yan kabilar Yi yara manyan gobe sun kunna wutar yola da ke hannunsu, su kan yi raye-raye a tituna. Bakin da suka shiga bikin kan rike da hannun juna, suna rawa tare da rera waka. Kowa da kowa na matukar murna. A can da, bikin mika wutar yola biki ne na gargaji da 'yan kabilar Yi kan shirya a kauyukansu. Amma sannu a hankali wannan bikin gargajiya na matsayin alamar yankin Shilin bisa bunkasuwar aikin yawon shakatawa na yankin Shilin. Don haka masu yawon shakatawa daga wurare daban daban na duniya sun je yankin Shilin domin shiga bikin mika wutar yola.

A lokacin da ake murnar bikin mika wutar yola, masu yawon shakatawa kan yi cunkuso a ko wane wurin yawon shakatawa da ke shiyyar Shilin. A rana, a kan yi gasar kokawa da gasa a tsakanin shanu. Dubu duban fararen hula na kabilu daban daban kan yi rawa da rera waka tare da sautin kida, sa'an nan kuma, su kan samar da abinci iri daban daban masu sigar musamman. Madam Zhang Yunlei, mataimakiyar shugaban hukumar aikin yawon shakatawa ta yankin Shilin, ta gaya mana cewa, hada al'adun kabilu da aikin yawon shakatawa tare ya kara inganta sigar musamman ta yankin Shilin a harkokin yawon shakatawa. Ta ce,

'Yankin Shilin ya dogara da aikin yawon shakatawa kawai a shekarun baya. Amma yanzu mun dora muhimmanci kan raya sauran fannonin da ke shafar aikin yawon shakatawa. Ga misali, mun hada al'adun kabilu da aikin yawon shakatawa tare, ta haka yankinmu wato Shilin ya kara inganta sigar musamman.'

Yankin Shilin da ke matsayin wurin tarihi na halitta na duniya ya zama daya daga cikin wuraren yawon shakatawa mafi shahara a duniya, mun yi imanin cewa, masu yawon shakatawa da ke fitowa daga ko ina a duniya za su ji farin ciki a wajen. (Tasallah)


1 2