Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-06 14:59:10    
Fahimtar yanayin al'adun kabilu a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin a kasar Sin

cri

Bikin mika wutar yola na gargajiya da 'yan kabilar Yi na kasar Sin suke yi wani gaggarumin biki ne na karamar kabila a yanki mai dimbin duwatsu wato Shili na lardin Yunnan na kasar Sin. In kun kai ziyara a yankin Shilin a karshen kwanaki 10 na watan Yuni zuwa farkon watan Yuli na ko wace shekara, to, za ku iya kara fahimtarku kan wannan kasaitaccen bikin gargajiya na kabilar Yi, tare da more idanunku da kyan karkara na halitta na wannan yanki.

A yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin, zuriyoyin 'yan kabilar Yi na aiki, suna shirya bukukuwan sadaukarwa, suna rera waka, suna raye-raye, sun kuma raya bikin mika wutar yola tasu zuwa mashahurin gaggarumin biki na kasashen duniyar gabas. Yawancin mutane sun san kabilar Yi bisa bikin mika wutar yola. Tun can da har zuwa yanzu, 'yan kabilar Yi na girmamawa wuta. Wata tsohuwar da ke zama a kauyen al'adun gargajiya na kabilar Yi da ke bakin tabkin Yuehu a yankin Shilin ta gaya mana cewa, a gun bikin mika wutar yola na ko wace shekara, a lokacin da dare ya yi duhu, mazaunan karkara sun kunna wutar yola da suka yi da rassan bihiyoyin pine, su kan yi yawo a tsakanin gonakinsu na noman shinkafa. Ta ce,

'A gun bikin mika wutar yola, mu kan kewaye gonakinmu tare da mika wutar yola domin nuna fatanmu na kashe dukkan kwari, ba za mu yi fama da bala'in kwari ba. Sa'an nan kuma, yanayi zai yi kyau a duk shekara mai zuwa.'

Bisa abubuwan da wannan tsohuwa ta fada, an ce, yin yawo a tsakanin gonaki tare da wutar yola a hannu kan kona kwari, ta haka za a tabbatar da girbin hatsi mai armashi a lokacin kaka. Tsoffafi kan yi amfani da wutar yolar da ta kuna domin gasa wakaikai ga dukkan iyalansu a bakin kofar gidajensu. Ci irin wadannan wakakai na iya tabbatar da kome da kome zai yi kyau a duk shekara. Anggui, wani saurayi, dan kabilar Yi, ya gaya mana cewa, a idanun 'yan kabilar Yi da ke zama a yankin Shilin, bikin mika wutar yola kasaitaccen biki ne. A daren ranar bikin, kowa de kowa kan ji matukar farin ciki har zuwa gari ya waye. Ya ce,

'A ranar da muka kaddamar da bikin mika wutar yola, kowa da kowa kan fita waje tare da wutar yola a hannu domin korar dodo. A ran 24 ga watan Yuni da dare bisa kalandar manoma ta kasar Sin, maza da mata, tsoffi da yara mun yi bikin carnival har duk dare. A rana kuwa, mu kan shirya gasa a tsakanin shanu da gasar kokawa da sauran harkoki.'


1 2