A shekarar bara, birnin Xuzhou ya zama daya daga cikin kyawawan birane 200 da ake sha'awarsu ainun a kasar Sin. Haka kuma a shekarar birnin ya kasance cikin sahon gaba a kasar Sin a fannin harkokin kudi. Saboda haka birnin ya zama kyakkyawan birnin da masu aikin masana'antu na kasashen waje ke sha'awar zuba masa jari.
Da Malam Xu Ming ya tabo magana a kan kudin jarin da birnin ke jawowa, sai ya yi marhabin da aminai na gida da waje da su zuba jari a birninsa don neman bunkasuwa. Amma ya gwada wasu abubuwan da masu zuba jari za su yi yayin da suke kafa masana'antu da yin ayyuka. Ya ci gaba da cewa, "da farko, muna maraba da masana'antun da za a kafa ba da ba su gurbata muhalli. Na biyu, muna maraba da kafa masana'antun wadanda za su kara samar da aikin yi mai yawa. Na uku, muna maraba da masana'antu na zamani wadanda muke nuna musu gatanci wajen zuba jari. Muna samar da kyawawan sharuda ga masu zuba jari a fannoni daban daban."
Birnin Xuzhou yana ta jawo hankulan 'yan kasuwa na kasashen waje da su zuba masa jari bisa kyakkyawan yanayinta na tattalin arziki da na zuba jari. Ya zuwa yanzu, akwai masana'antu mafi girma 500 a duniya wadanda suka yi ayyuka 17 bisa jarinsu a birnin Xuzhou, jimlar kudin jari da suka zuba ya wuce dalar Amurka miliyan 600. Yanzu, ana kara bunkasa harkokin tattalin arzikin birnin Xuzhou ta hanyar jawo makudan kudaden jari daga kasashen waje da kyakkyawar hanyar da ake bi wajen kulawa da aikin samar da kayayyaki. (Halilu) 1 2
|