Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-05 20:22:58    
Ana raya birnin Xuzhou na kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba

cri

Birnin Xuzhou yana arewa maso yammacin lardin Jiangsu da ke a bakin teku na gabashin kasar Sin. Birnin muhimmin birni ne da ke samar da albarkatu da makamashi a lardin Jiangsu, haka kuma shi ne kadai sansanin hakar kwal a lardin. A bangare guda, ana amfani da makamashi mai yawa da ake samu a birnin wajen gaggauta bunkasa aikin masana'antu na birnin Xuzhou, a daya bangare kuma an kawo illa ga muhallin birnin. Da malam Xu Ming, sakataren reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a birnin Xuzhou ya tabo magana a kan yadda ake daidaita batun kiyaye muhalli da na bunkasa tattalin arziki, sai ya bayyana cewa, "ko shakka babu, muna kiyaye muhalli yayin da muke bunkasa harkokin tattalin arzikin birninmu."

Ba ma kawai Mr Xu ya fadi haka ne ba, har ma ya jagoranci mazaunan birninsa da su yi haka. Gwamnatin birnin Xuzhou ta yi kokari sosai wajen kyautata muhalli. Ya kara da cewa, "birnin Xuzhou wurin hakar kwal ne, kana kuma shi ne muhimmiyar mahadar hanyoyin zirga-zirgar jiragen kasa. Sabo da haka a cikin wani dogon lokaci da ya wuce, in wani ya shiga cikin birnin, sai ya kan shaki kura mai yawa. Ganin haka, ya sanya muka daina yin amfani da murahu masu aiki da kwal a duk birnin a cikin shekarun nan biyu da suka wuce, yanzu muna amfani da gas ba tare da gurbata muhalli ba. Kana kuma mun dauke masana'antun harhada sunadarai daga birnin, ta yadda za a samar da kyawawan sharuda ga kiyaye muhallin duk birnin."

An ruwaito cewa, birnin Xuzhou ya rufe kananan masana'antun sumunti da yawansu ya kai 47, da kananan masana'antun yin takardu da yawansu ya kai 117, sa'an nan ya rufe duk kananan wuraren hakar kwal, ya rushe murahun 646 da bututun hayaki da yawansu ya kai 740 a cibiyarta. Bayan haka an kara kyautata yanayin iska a birnin cikin shekaru da yawa da suka wuce a jere.

Malam Xu Ming yana ganin cewa, ruwa da bishiya muhimman abubuwa biyu ne ga muhallin birane. Saboda haka birnin Xuzhou ya yi kokari sosai wajen kiyaye muhallin ruwa a cikin shekaru biyu da suka wuce, kana kuma ya rubanya kokari wajen dashe-dashen bishiyoyi. Yanzu, matsakaicin fadin bishiyoyi da na ciyayi da ko wane mazaunin birnin Xuzhou ke da shi ya kai misalin muraba'in mita 8, shingen bishiyoyi na birnin ya kai kashi 23 cikin dari, ya kai matsayi na farko a duk lardin Jiangsu baki daya.

1 2