Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-05 17:59:07    
Condoleeza Rice tana sha wuyar samun cigaba a yankin Gabas ta tsakiya

cri

Manazarta sun nuna cewa, gwamnatin Bush ta Amurka ta sa taron kasa da kasa na batun yankin Gabas ta tsakiya a matsayin tamkar abin koyi na aiwatar da manufofinta na yankin Gabas ta tsakiya. Har yanzu, ba ta daidaita batun Iraki ba, batun nukiliya na Iran ma ya dame ta sosai. A cikin irin wannan halin da take ciki, idan ba za ta iya samun ci gaba ba daga wajen ayyukan shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, mai yiyuwa ne manufofin da gwamnatin Bush take aiwatarwa a yankin Gabas ta tsakiya za su sha kaye. Wannan shi ne muhimmin dalilin da ya sa gwamnatin Bush ta ba da shawarar shirya taron kasa da kasa na yankin Gabas ta tsakiya, kuma tana fatan za a samu nasara a gun wannan taro. Amma idan kasar Amurka ba za ta canja hanyarta ba, kasar Isra'ila ba za ta cimma tudun dafawa ba kan muhimman batutuwan da ke shafar huldar da ke tsakaninta da Palesdinu. Sabo da haka, ko da yake madam Rice ta kai ziyara a yankin Gabas ta tsakiya har sau da yawa, amma za a sha wuyar samun cigaba a gun taron kasa da kasa na yankin Gabas ta tsakiya da za a yi. (Sanusi Chen)


1 2