Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-05 17:59:07    
Condoleeza Rice tana sha wuyar samun cigaba a yankin Gabas ta tsakiya

cri

A ran 4 ga wata, Condoleeza Rice, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka ta isa birnin Kudus domin fara ziyara ta kwanaki 2 a kasashen Isra'ila da Palesdinu. Wannan ne karo na 8 a cikin tsawon shekara 1, kuma karo na 3 ne a cikin makonni 6 da suka wuce da ta kai ziyara a yankin Gabas ta tsakiya. Amma manazarta sun nuna cewa, kamar sauran ziyarce-ziyarce da yawa da ta taba yi a wannan yanki, ziyarar da madam Rice take yi yanzu a yankin ba za ta samu hakikanin cigaba ba.

Ana iya gano irin wannan halin da ake ciki domin labaru game da wannan ziyarar Condoleeza Rice da kafofin watsa labaru na wurin suka bayar sun yi kama da labarun da suka bayar lokacin ziyarar da Condoleeza Rice ta yi a karon da ya gabata. Makasudin wannan ziyara yana kama da na wancan ziyara, wato "kara saurin sassauta sabanin da ke kasancewa a tsakanin Palesdinu da Isra'ila da kuma samun ra'ayi daya kan hadaddiyar sanarwar da ake shiryawa kafin taron kasa da kasa kan batun yankin Gabas ta tsakiya." A waje daya kuma, kafin ta tashi daga Amurka zuwa yankin Gabas ta tsakiya, Condoleeza Rice ta kuma bayyana cewa, kada a sa ran cewa za a iya samun babban cigaba ta wannan ziyara daya kadai domin batun yankin Gabas ta tsakiya yana da sarkakiya sosai. Dole ne a daidaita wannan batu sannu a hankali. Kuma har yanzu, dalilan da suka sa ba a iya daidaita batun ba su ne, sabane-sabanen da suke kasancewa a tsakanin bangarorin biyu kan muhimman matsaloli, kamar su matsalar kan iyakar da ke tsakanin Palesdinu da Isra'ila da ikon komar da 'yan gudun hijira na Palesdinu da matsayin da birnin Kudus ke ciki. Har yanzu, bangaren Palesdinu ya nemi a daddale wata yarjejeniya game da wadannan batutuwa, kuma a tabbatar da hakikanin lokacin kafa kasar Palesdinu. Amma bangaren Isra'ila ya nemi a bayar da wata sanarwa mai kunshe da wasu muhimman ka'idoji kawai game da wadannan batutuwa. Sabo da haka, kafofiin watsa labaru na wurin sun ce, ziyarar da madam Rice take yi a yankin Gabas ta tsakiya ba ta da sabon mataki ban da karuwar yawan yin ziyara a yankin.

Manazarta sun nuna cewa, a hakika dai, an shiga cikin irin wannan hali ne domin ya kasance da matsaloli iri iri a gun shawarwarin da yake shafar wadannan muhimman batutuwa. Sabo da haka, duk irin hanya ko matakin da za a dauka lokacin da ake bayar da hadaddiyar sanarwa, dole ne a tabbatar da ka'idoji domin shirya shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Palesdinu da daidaita batun kafa kasar Palesdinu. Amma yanzu, bangarorin biyu sun gane cewa, ba zai yiyuwa ba su kau da sabane-sabanen da ke tsakaninsu ta wani taro kawai. A waje daya kuma, yaya za a tabbatar da wadannan muhimman ka'idoji zai yi tasiri ga saurin yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya. Wannan matsala ce mafi muhimmanci da take shafar babbar moriya ta bangarorin nan biyu. Kuma idan ana son daidaita su, dole ne bangarorin biyu su cimma tudun dafawa duka. Wannan na daya daga cikin muhimman dalilan da suka sanya aka rubuta wasu kalmomi kadai a cikin hadaddiyar sanarwar da aka soma shiryawa domin taron kasa da kasa na batun yankin Gabas ta tsakiya bayan da aka soma yin shawarwari a birnin Kudus tun daga ran 8 ga watan Oktoba.

1 2