Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:23:55    
Ingancin amfanin gona na kasar Sin ya kara samun kyautatuwa

cri
 

Aikin kyautata ingancin amfanin gona ya inganta kyautatuwar matsayin sa ido kan amfanin gona na wurare daban daban na kasar Sin. Lardin Shandong wani lardi ne mai girma wajen fitar da amfanin gona zuwa waje, yawan amfanin gona da yake fitarwa zuwa kasashen waje a ko wace shekara ya kai kusan sulusi na duk kasar Sin. Bayan da aka kaddamar da aikin, lardin Shandong ya gaggauta kafa tsarin binciken ingancin aikin gona, da kuma kyautata sauran tsare-tsare uku da abin ya shafa, ta haka yawan amfanin gonar da suke da inganci ya samu karuwa a bayyane. Li Zhanxiang, mataimakin shugaban sashen aikin gona na lardin ya bayyana cewa,

"lardin Shandong ya samu sakamako mai kyau a fannin ingancin amfanin gona, yanzu yawan amfanin gona da aka amince da su a cikin binciken da aka gudanar a kansu domin gwajin mummunan sinadarin da suka yi saura cikinsu a duk fadin lardin ya riga ya kai fiye da kashi 96 cikin dari. Ban da wannan kuma mun gaggauta kafa tsare-tsaren sa idon kan ingancin amfanin gona iri daban daban, ya zuwa yanzu an riga an kafa cibiyoyin binciken ingancin amfani gona fiye da 100 a hukumomin aikin gona a gundumomi da kuma biranen lardin."

Ko da yake aikin kyautata ingancin amfanin gona ya samu sakamako mai kyau, amma Mr. Gao ya nuna cewa, ana kasancewa da matsalar rashin daidaito a wurare daban daban. Sabo da haka, a nan gaba, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da kara karfin duddubawa da kuma kafa wani tsarin tabbatar da ingancin amfanin gona na dogon lokaci domin ci gaba da kyautata ingancinsu. Kuma ya kara da cewa,

"aikin kyautata ingancin amfanin gona wani aiki ne da aka gudanar a wani lokaci, shi ya sa za mu mai da hankali a kan kafa wani tsari na dogon lokaci. Ban da wannan kuma za mu kara karfin horar da manoma domin su kara fahimtar ma'anar ingancin amfanin gona. Idan an kafa tsari na dogon lokaci, to za a iya tabbatar da ingancin amfanin gona mai dorewa, ta haka za a iya ba da tabbaci ga ingancin amfanin gona a fannin dokoki."


1 2