Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:23:55    
Ingancin amfanin gona na kasar Sin ya kara samun kyautatuwa

cri

Mataimakin ministan aikin gona na kasar Sin Gao Hongbin ya yi bayani a ran 29 ga wata a birnin Beijing, cewa aikin kyautata ingancin amfanin gona da kasar Sin ta gudanar tun watan Satumba na shekarar da muke ciki ya samu sakamako mai kyau a bayyane, kuma ingancin amfanin gona ya kara samun kyautatuwa. Kuma ya bayyana cewa, a galibi dai, amfanin gona na kasar Sin suna da inganci, kuma ana iya kwantar da hankali wajen cinsu. A nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga ayyuka daban daban da abin ya shafa domin daga matsayin ingancin amfanin gona zuwa wani sabon mataki. To, yanzu ga cikakken bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana.

Ana gudanar da aikin musamman na kyautata ingancin amfanin gona a duk fadin kasar Sin daga watan Satumba zuwa watan Disamba na shekarar nan domin tabbatar da ingancin amfanin gona ta hanyar bin tushensa. Mataimakin ministan aikin gona na kasar Sin Gao Hongbin ya yi bayani a gun taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran nan, cewa a watannin nan biyu da suka gabata, an aika da jami'an da suke tabbatar da doka da yawansu ya zarce dubu 300 zuwa wurare daban daban domin kyautata ingancin amfanin gona, kuma an samu sakamako mai kyau. Ya kara da cewa,

"Bisa sakamakon binciken da ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ta yi wa kasuwanni 100 na sayar da amfanin gona na sari a 'yan kwanakin nan da suka gabata, an ce, yawan kayayyakin lambu da aka amince da ingancinsu a cikin binciken da aka gudanar a kansu domin gwajin magungunan kashe kwari da suka yi saura a cikinsu ya kai fiye da kashi 94 cikin dari, kuma yawan kayayyakin dabobi da aka amince da ingancinsu a cikin binciken da aka gudanar a kansu ya zarce kashi 99 cikin dari, haka kuma yawan kayayyakin ruwa da aka amince da ingancinsu a cikin binciken da aka gudanar a kansu domin gwajin magungunan da suka yi saura a cikinsu ya kai fiye da kashi 95 cikin dari."

Ban da wannan kuma Mr. Gao ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu an riga an shigar da kasuwannin sayar da abinci na sari na manya da matsakaitan birane 676 na kasar Sin cikin tsarin duddubawa.


1 2