Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-26 19:16:00    
Gyararren tsarin mulkin JKS ya nuna kyakkyawan halin jam'iyyar, wato sarrafa lokacin da ake da shi kamar yadda ya kamata

cri

Bugu da kari kuma, abin da aka lura da shi shi ne a cikin gyararren tsarin mulkin jam'iyyar, an yi bayani kan inganta dimokuradiyya a cikin jam'iyyar da kuma kyautata tsarin jam'iyyar. Game da wannan, malam Yan ya kara da cewa,'A cikin rahoton da aka gabatar a gun babban taron, an dora muhimmanci kan kyautata tsari a fannin raya jam'iyyarmu. Ban da wannan kuma, an dora muhimmanci kan yaki da cin hanci da rashawa a harkokin kyautata tsarin jam'iyyar. Ayyukan gaskiya da muka yi a shekarun baya sun shaida cewa, wadannan tsare-tsare na da amfani sosai, tanadensu cikin tsarin mulkin jam'iyyar na ba da taimako sosai, za su daukaka yada dimokuradiyya ta gurguzu, musamman ma a cikin jam'iyyarmu.'

A cikin shekaru 25 da suka wuce, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta yi kwaskwarima kan tsarin mulkinta sau 5. Tsarin mulkin jam'iyyar da aka yi masa gyare-gyare ya nuna sabon sakamakon da jam'iyyar ta samu wajen raya tunanin Markisanci bisa halin da kasar Sin ke ciki. Malam Yan ya ci gaba da cewa, gyare-gyaren da jam'iyyarmu ta yi wa tsarin mulkinta sun nuna cewa,'Abubuwan gaskiya na samun ci gaba, haka kuma, tarihi ya sami ci gaba. Kuma tunanin jagoranci na jam'iyyar ya sami ci gaba bisa lokacin da muke ciki. Tsarin mulkin jam'iyyarmu kan nuna sakamakon da ta samu daga ayyukan gaskiya da kuma nasarar da ta samu a fannin tunani.'(Tasallah)


1 2