A gun babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 da aka rufe ba da dadewa ba, an zartas da daftarin tsarin mulkin jam'iyyar, wanda aka tanada tunanin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya da kuma tsarin tunanin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a ciki. Kwararrun kasar Sin masu ilmin raya jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin sun nuna cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta sarrafa lokacin da ake da shi kamar yadda ya kamata a fannin kyautata tunanin jagoranci. Gyararren tsarin mulkin jam'iyyar zai ba da babban tasiri kan bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasasrmu.
Malam Yan Shuhan, darektan sashen nazarin gurguzu na kimiyya na jami'ar ilmin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na tsakiya na kasar Sin, ya ce, sabon abu mafi muhimmanci da gyararren tsarin mulkin jam'iyyarmu ya nuna a fannin manyan tsare-tsare da tunani shi ne tanadi? aiwatar da tunanin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya yadda ya kamata a ciki. Ya kuma jaddada cewa,'Muhimmiyyar ma'anar tanada tunanin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya a cikin tsarin mulkin jam'iyyarmu shi ne za mu ci gaba da gwagwarmaya bisa irin wannan muhimmin tunani a cikin shekaru 5 zuwa 13 masu zuwa. Jam'iyyarmu jam'iyya ce kacal da ke mulkin kasar Sin cikin dogon lokaci, shi ya sa makasudin da jam'iyyarmu ta tsara kan ba da babban tasiri kan kasarmu da al'ummarmu. An tanadi tunanin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya cikin tsarin mulkin jam'iyyar a matsayin manyan tsare-tsare da tunani da tilas ne a nace ga binsu da aiwatar da su a fannin raya gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin. Ta haka za a ba da jagoranci da kayyadewa kan shugabanninmu a matakai daban daban da kuma 'yan jam'iyyar fiye da miliyan 70.'
Tanada tunanin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya cikin tsarin mulkin jam'iyyar ya sami goyon baya daga wakilai masu halartar babban taron. Malam Qizhala, wani daga cikinsu, yana ganin cewa, tunanin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya na amfanawa wajen warware batutuwa da matsalolin da kasar Sin ke fuskanta domin samun ci gaba a yanzu. Ya ce,'Tanada tunanin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya cikin tsarin mulkin jam'iyyarmu, an kuma mayar da shi a matsayin muhimmin bangaren tunanin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin. Tabbas ne zai ba da taimako wajen kafa zaman al'ummar kasar Sin mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni a nan gaba, da kauce wa hanyar da ba ta dace ba, da warware matsalolin da ake fuskanta a fannin samun ci gaba, da kuma gudanar da ayyuka yadda ya kamata da idon basira.'
1 2
|