
Madam Wurengerile, wata mace ce daban mai kula da harkokin kauyen E'erdengbaolige wadda shekarunta ba su kai 50 ba da haihuwa ta taba zama direktar kwamitin mata na wannan kauye. A yayin da ta tabo magana kan ayyukan da ta yi bisa matsayinta na direktar kwamitin mata na kauyen ta bayyana cewa, "A wancan lokaci, yawan yaran da suka isa shiga makaranta wandanda kuma aka shigar da su kadan ne, sabo da haka, muhimmin aikinmu shi ne mu yi furofaganda ga mata don fadakar da su da su aika da yaransu zuwa kamaranta don samun ilmi. Yanzu, tunanin mutane ya sauya, yaran da suke yin karatu cikin makaranta sun karu da yawa. Cikin wadannan shekaru 2 da suka wuce, da akwai 'yan makaranta su 3 na kauyen Gacha da suka ci jarrabawa har sun shiga cikin jami'a wato sun zama dalibai. Ban da wannan kuma, kwamitin mata ya jagoranci mata a fannonin aikin kawo albarka da zaman rayuwarsu. Yanzu, mata da yawa wadanda suke kiwon dabbobi ta hanyar kimiyya. Direktar kwamitin mata ta yanzu ita ma mu ne muka yi mata tallafi. Mata ne suka taka rawa sosai cikin iyalai masu arziki da wadata.

Madam Wurengerile ta kuma bayyana cewa, a filayen ciyayi wato a wuraren kiwon dabbobi, mata sukan yi ayyuka da yawa. A da mata sun sha aiki tun safe har zuwa dare na kowace rana, amma mijinsu sun yi aiki kadan, sukan yi zaman nishadi, amma mata ba su shiga cikin su. Yanzu yanayi ya sauya wato maza ma suna ba da taimako ga yin aikace-aikacen gida. A gun gagarumin bikin da ake kira "Nadamu" da 'yan kabilar Mongoliya sukan yi sau daya a shekara, akan iya ganin mata da yawa wadanda suka shiga cikin wasanni da yawa ciki har da wasan kokawa da harba kibiya da sukuwar dawaki. 1 2
|