Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 16:48:37    
Mata 'yan kabilar Mongoliya da ke filin ciyayi na Xilinguole

cri

Madam Tuoya wata mace 'yar kabilar Mongoliya ce kamar kowa da ke filin ciyayi na Xilinguole wadda shekarunta 30 ne da haihuwa, fuskarta na cike da annuri. Ta bayyana cewa, "Nakan tashi daga barci a kowace rana da karfe 5 na safe, daga bisani kuma na fara yin kayayyakin nono domin 'yan iyalina. A rana kuma nakan tatsa nonon godiyoyi sau daya a kowadanne sa'o'i 2, wato nakan yi wannan aiki sau 6 a kowace rana."

Kafin madam Tuoya ta yi aure, ta riga ta saba da yin wadannan aikace-aikacen gida. Yanzu kuma tana renon danta mai shekaru 6 da haihuwa a kowace rana, tana nan tana yin haka a kwana a tashi.

Dagaci mace na kauyen E'erdengbaolige mai suna E'erdeng'gerile, wadda take da mutane 5 a gidanta, wato ban da mijinta kuma akwai surukinta da surukarta da kuma danta mai shekaru 2 da rabi da haihuwa. Bisa yawan 'yan iyalinta, gidanta ta samu filin ciyayi mai fadin kadada 600 ko fiye. Madam E'erdeng'gerile ta bayyana cewa, "A shekarar 1983 zuwa ta 1984, an rarraba dabbobin gida ga kowane iyali, daga shekarar 1991 kuma an fara rarraba wa makiyaya filayen ciyayinsu."

Yawan dabbobin gida da duk 'yan iyalin E'erdeng'gerile suke kiwon su ya kai fiye da 600, ciki har da tumaki 400 da shanu 200 ko fiye. Bayan da suka sayar da kanana shanu da tumaki da kuma gashin tumaki, sukan samun kudin shiga da yawansu ya kai kusan kudin Sin Yuan dubu 100 a kowace shekara, wato yawan kudin da suka samu ya kai matsakaicin matsayi ko fiye da haka a wannan wuri.

1 2