
'Yan kabilar Tajik suna son yin wake-wake da raye-raye sosai, sukan yi wake-wake da raye-raye a duk lokutan da suke yin bukukuwan gargajiya ko bikin sabuwar shekara ko kuma bikin aure. Mutane maza da mata, manya da kanana dukkansu sun gwanance wajen yin rawa da waka. A hakika kuwa, 'yan kabilar Tajik da ke zama kan faffadan tsaunin Pamir ba ma kawai sun iya waka da rawa ba, kuma suna da karfin zuciya don kare mahaifarsu. Faffadan tsaunin Pamir yana da dogon layin iyakar kasa, a cikin shekara da shekaru da suka wuce, manoma da makiyaya 'yan kabilar Tajik sun dauki nauyin taimakawa sojojin tsaron iyakar kasa don tsaron kasar bisa radin kansu. A kan kololuwan duwatsu da ke rufe da dusar kankara, a duk lokutan da sojojin tsaron iyakar kasa suka gamu da wahaloli bisa hanyarsu ta yin zintiri, sai makikiya 'yan kabilar Tajik sukan fito fili don ba su taimako. Mr. Moni Tablit, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na gundunar Tashiku'ergan ya taba cewa haka,

"Cikin shekaru 2,000 da suka wuce, gudumawa mafi girma da 'yan kabilar Tajik suka bayar ga kasar mahaifarsu ita ce kare bakin iyakar kasa, 'yan kabilar Tijik suna nuna kyayyawan tunanin kishin kasa sosai, suna son kasar mahaifa da kuma garinsu, ko kusa ba su tashi daga kasar mahaifarsu ba, maimakon haka kuma suna ba da taimako ga sojoji masu sintiri don kare bakin iyakar kasa na kasar Sin."(Umaru) 1 2
|