Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 15:33:21    
'Yan kabilar Tajik da ke kan faffadan tsaunin Pamir

cri

Ya kasance da kololuwan duwatsu 14 wadanda tsayinsu ya wuce mita 8000 da ke kan faffadan tsaunin Pamir na Asiya, nan ne ake kiran shi da suna "kakani-kakanin duwatsun duniya". Cikin shirinmu na yau, za mu zagaya da ku faffadan tsaunin Pamir da ke kudu maso yammacin jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin don ganin yadda 'yan kabilar Tajik wadanda ake kiran su da suna "Shahunan Pamir" suke yin zama a can.

Da akwai wasu kananan kabilu ciki har da kabilar Tajik da Uighur da Ke'erkezi da Hui wadanda suke zama a kan faffadan tsaunin Pamir, daga cikin su kuma yawan 'yan kabilar Tajik ya kai kusan kashi 90 bisa 100, kuma yawancinsu suna zama a gundumar Tashiku'ergantajik mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta jihar Xinjiang. A da 'yan kabilar Tajik sun mai da muhimmanci kan aikin kiwon dabbobi, sa'an nan kuma sun yi aikin noma. Bayan kafa sabuwar kasar Sin, an kafa gundumar Tashiku'ergantajik mai ikon tafiya da harkokin kanta a shekarar 1954. Bisa babban goyon bayan da gwamnatin kasar Sin ta nuna mata ne, kabilar Tajik ta sami ci gaba da sauri wajen tattalin arziki, zaman rayuwar jama'a ya samu kyatatuwa a bayyane, sabo da haka kabilar ta shiga cikin wani sabon lokacin tarihi.

'Yan kabilar Tajik sun kago al'adu masu sigar musamman na kansu, bukukuwan gargajiya na kabilar sun zama wani muhimmin kashi ne daga cikin dabi'unsu. 'Yan kabilar Tajik suna bin addinin musulunci, sabo da haka su ma suna yin bikin gargajiya wato babbar salla. Ta yaya mutane 'yan kabilar Tajik suke yin babbar salla? Mr. Ebuli, mai ba da labari na wurin ya ba wa wakilinmu amsar wannan tambaya cewa,

"Akan yanka raguna a lokacin babbar salla, kuma akan zabi ragunan da za a yanka tun bayan haihuwar su a farkon lokacin sabuwar shekara, launinsu fari ne fat. Yanke raguna aiki ne mai tsarki, shi ya sa akan dauki raguna zuwa kan rufin dakuna, sa'an nan an yanke su."


1 2