
Mr. Wu ya kuma fadi cewa, " Ban da babban filin wasa na kasar Sin da kauyen kafofin yada labaru da kuma gine-ginen dake shafar tarurrukan wasannin, za a kuma kammala gina sauran filaye da dakunan wasa da gine-ginen da abin ya shafa a karshen wannan shekara daya bayan daya".

Dadin dadawa, a lokacin da ake gina filaye da dakunan wasan, ana bin tunanin " shirya taron wasannin Olympic ta hanyar kimiyya da fasaha ta zamani, tare kuma da mai da hankali kan al'adu da kiyaye muhalli". Yanzu, an samu sakamako mai faranta rai wajen gudanar da ayyukan dake shafar taron wasannin Olympic a fannin tsara shiri gaba daya, da yin tsimin albarkatun ruwa da kuma yin amfani da sabon makamashi da dai sauransu".
Aminai 'yan Afrika, yin amfani da wadannan filaye da dakunan wasa bayan taron wasannin Olympic na Beijing, shi ma ya yi ta janyo hankalin kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sosai. Domin magance dakatar da yin amfani da su da kuma bata albarkatu bayan taron wasannin Olympic na shekarar 2008, wannan kwamiti ya kaddamar da shirye-shirye iri daban-daban don tabbatar da matukar amfanin wadannan filaye da dakunan wasa. Mr. Wu ya yi karin haske cewa, hukumar Beijing ta raya wadannan filaye da dakunan wasa kamar yadda ya kamata bayan taron wasannin Olympic na Beijing duk bisa bambancinsu da kuma sigogin musamman nasu. Ga misali: filaye da dakunan wasa da aka gina a wasu jami'o'I da kolejoji za su zama cibiyoyin wasannin motsa jiki ga dalibai da matasa. Sa'annan kuma, 'yan kasuwa za su zuba jari kan wadanda aka gina domin dalilin kasuwanci; kuma za a shirya manyan gasanni da kuma kasaitattun wasannin kide-kide a wadannan filaye da dakunan wasa. ( Sani Wang ) 1 2
|