An labarta cewa, a gun taron manema labaru da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kira a kwanakin baya ba da dadewa ba, wani jami'in kula da ayyukan taron wasannin Olympic na Beijing kuma babban injiniya na ofishin bada jagoranci ga gudanar da harkokin taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing Malam Wu Jinjun ya yi wa kafofin yada labaru karin bayanin cewa, yanzu haka, ana gina filaye da dakunan wasanni domin taron wasannin Olympic na Beijing kamar yadda ya kamata. Bayan da aka soma gina filayen wasa guda biyu na wucin gadi wato na wasan Triathlon dake kunshe da wasan iyo, da wasan gudun fanfalake da wasan tseren keke da kuma na tseren keke kan hanyar mota a shekarar da muke ciki, gwamnatin birnin Beijing ta fara gina dukkanin filaye da dakunan wasa guda 31 da kuma gine-gine guda 5 da a bin ya shafa. Sa'annan kuma, ta soma gina wasu 43 daga cikin dukkan filaye da dakunan wasa guda 45 masu zaman kansu domin aikin horaswa.
Mr. Wu ya ci gaba da cewa, " Beijing ta kaddamar da shirin gina dukkan filaye da dakunan wasa guda 31 da kuma gine-gine guda 5 da abin ya shafa. Ban da filin wasan kwallo mai laushi na Fengtai da ta kammala gina shi a shekarar bara, yanzu ta rigaya ta kawo karshen gina yawancin muhimman gine-gine na wadannan filaye da dakunan wasa da kuma gine-ginen da abin ya shafa. Yanzu ma'aikata suna kayatar da su da kuma harhada injunan wutar lantarki a cikinsu".
Kazalika, Mr. Wu ya fadi, cewa a cikin filaye da dakunan wasa guda 31 domin taron wasannin Olympic na Beijing, guda 12 daga cikinsu ne aka soma harhada injunan wutar lantarki a ciki. A cikin filaye da dakunan wasa guda 11 da ake yi musu kwaskwarima, an rigaya an kammala gina filin wasan kwallo mai laushi na Fengtai, saura guda 10 kuma, yanzu ana kusan kammala gina su. Dadin dadawa, an kaddamar da ayyukan gina filaye da dakunan wasa guda 8 na wucin gadi duka. Dangane da lokacin da za a kammala gina dukkan filaye da dakunan wasa, Mr. Wu ya bayyana cewa, za a kammala ayyukan yawancin wadannan filaye da dakunan wasa ne kafin karshen shekarar da muke ciki.
1 2
|