Wasu kafofin watsa labaru suna ganin cewa, muhimmin dalili daban da ya bayyana cewa ziyarar da Sarkozy ya kai wa kasar Rasha "ba ziyayar banza ba ce" shi ne huldar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasashen biyu ta kuma samu cigaba. Faransa da Rasha suna hadin guiwa sosai a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Kasar Faransa muhimmiyar abokiyar cinikayya ce ta kasar Rasha. Ya kasance da muhimmin ayyukan hadin guiwa a fannonin zirga-zirgar sararin sama da albarkatun halittu a tsakaninsu. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, saurin karuwar yawan kudaden cinikayya a tsakaninsu ya kai kashi 30 zuwa kashi 40 daga cikin kashi dari a kowace shekara. Jimlar kudaden cinikayya da aka yi a tsakaninsu ya riga ya kai dala biliyan 13.5. Yanzu, kamfanin Total na Faransa da kamfanin masana'antun man gas na Rasha suna hako filayen man gas tare a kasar Rasha.
A waje daya, manazarta sun nuna cewa, ko da yake ziyarar da Mr. Sarkozy ya kai wa kasar Rasha ta samu wasu sakamako, huldar da ke tsakanin Faransa da Rasha ta kai wani sabo mataki, amma domin matsayin da kasashen nan biyu suke dauka kan wasu muhimman batutuwan kasa da kasa yana da bambanci sosai, dole ne bangarorin biyu sun ci gaba da yin kokari domin kara raya huldar da ke tsakanin Rasha da Faransa. (Sanusi Chen) 1 2
|