Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-11 16:51:58    
Ziyarar shugaba Sarkozy na Faransa a kasar Rasha da huldar da ke kasancewa tsakanin kasashen biyu

cri

Tun daga ran 9 zuwa ran 10 ga wata, shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa ya kai wa kasar Rasha ziyarar aiki ta kwanaki 2. Wannan ne karo na farko da Mr. Sarkozy ya kai wa kasar Rasha ziyara bayan da ya hau kan mukamin shugaban kasar Faransa. Lokacin da yake ziyara a kasar Rasha, shi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun tattauna kan batutuwa yadda za a yi hadin guiwa a tsakanin kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da zuba jari da "yarjejeniyar rundunonin soja na yau da kullum na Turai" da shirin kafa tsarin maganin makamai masu linzami a kasashen gabashin Turai da kasar Amurka take aiwatarwa da batun Kosovo da na halin da ake ciki a yankin Gabas ta tsakiya da halin da ake ciki a kasar Iraki da shirin nukiliya na Iran da taron koli na Rasha da kungiyar Tarayyar Turai da za a yi a kasr Portugal a karshen wannan wata da dai makamatansu.

Bayan da ya hau kan mukamin shugaban kasar Faransa a watan Mayu na shekarar da muke ciki, sau da dama ne Mr. Sarkozy ya zargi kasar Rasha. Sakamakon haka, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ba ta da kyau a cikin 'yan watannin da suka gabata. Saboda haka, wasu kafofin watsa labaru sun bayyana cewa, Mr. Sarkozy ya kai wa kasar Rasha ziyara ne domin kokarin gyara huldar da ke tsakanin Faransa da Rasha.

Manazarta sun gane cewa, ko da yake huldar da ke tsakanin kasashen biyu ba ta da kyau, amma Mr. Putin da Mr. Sarkozy dukkansu sun musunta magana wai huldar da ke tsakanin kasashen biyu tana cikin mawuyacin hali, kuma a fili ne sun jaddada cewa huldar da ke tsakanin kasashen biyu tana da muhimmanci sosai. Lokacin da suke shawarwari, Mr. Putin ya gaya wa Sarkozy cewa, tun a da, ko a yanzu, ko a nan gaba, kasar Faransa muhimmiyar abokiya ce ta kasar Rasha a Turai. A gun wani taron manema labaru da aka shirya bayan shawarwarin, Mr. Sarkozy ya gaya wa manema labaru cewa, ko da yaka ya kasance da wasu ra'ayoyi daban kan wasu batutuwa, amma bangarorin biyu dukkansu suna fatan za a kara yin hadin guiwa da raya hulda a tsakaninsu. Wannan yana da muhimmanci sosai bayan da kasar Rasha ta koma dandalin siyasa na duniya. Yana ganin cewa, dukkan kasashen duniya za su samu moriya daga hadin guiwar da ake yi a tsakanin Turai da Rasha. A gun shawarwarin, shugabannin nan biyu dukkansu suna fatan za a kara raya huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Saboda haka, ana ganin cewa, ziyarar da Sarkozy ya kai wa kasar Rasha domin gyara huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta samu sakamakon da ake fata, kuma ta ciyar da huldar da ke tsakanin Faransa da Rasha gaba.

1 2