Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 16:08:03    
Kiyaye ikon mallakar ilmi a matsayin sabuwar manufar da ake bi wajen bunkasa kasashe masu tasowa

cri

Mahalartan taron kuma suna ganin cewa, hakika, wajibi ne, kasashe masu tasowa su yi ta kara kwarewa wajen yin kirkirawa, amma yanzu, gibin da ke tsakanin arewa da kudu kullum sai kara karuwa yake yi, wannan ma hakikanin abu ne da ba a musanta shi ba. Malam Makarim Wibisono, jakadan kasar Indonesiya a kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ya bayyana cewa, akwai matsaloli da yawa da wajibi ne kasashe maso tasowa su daidaita su a gaba. Ya kara da cewa, "da aka tabo magana a kan batun ikon mallakar ilmi, wajibi ne. a kiyaye ikon mallakar ilmi, sa'an nan a kula da sauran abubuwa da yawa na ba da ilmi da kiwon lafiya da tushen tattalin arziki da sauransu. Batun zaman rayuwar jama'a wani babban batu ne da ya kamata gwamnatocin kasashe su daidaita shi tun da farko."

Yayin da ake tattaunawa a gun taron, kasashe masu tasowa da yawa sun lura da matsi da kasar Sin ke sha a wasu fannoni a kwanan nan. Yayin da Malam Zhao Meisheng , jami'in hukumar kula da harkokin ikon mallakar ilmi ta kasar Sin ya nuna adadai masu yawa cewa, kasar Sin ta yi kokari sosai wajen kare ikon mallakar ilmi bisa doka kuma ta sami kyakkyawan sakamako. (Halilu)


1 2