Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 16:08:03    
Kiyaye ikon mallakar ilmi a matsayin sabuwar manufar da ake bi wajen bunkasa kasashe masu tasowa

cri

A cikin wani tsawon lokaci da ya wuce, wani sabon batun da ke jawo hankulan mutane sosai, shi ne kasashe masu sukuni sun sha kyamar kasashe masu tasowa bisa sanadiyyar surutun baki na wai rashin kiyaye ikon mallakar ilmi da kyau. Yanzu, ikon mallakar ilmi ya riga ya zama sabon abin toshewar fasaha. A ran 9 ga wannan wata, a birnin Geneva, cibiyar kudu ta kungiyar gwamnatocin kasashe masu tasowa ta shirya taron tattaunawa musamman domin neman daidiata wannan batu.

An shirya wannan taron tattaunawa ne a daidai lokacin da kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO da kungiyar kiyaye ikon mallkar ilmi ta duniya za su fara yin sababbin shawarwari kan ikon mallakar ilmi. Taron ya gayyaci shahararrun masanan ilmi na duniya don su bayyana halin da ake ciki dangane da aiwatar da ikon mallakar ilmi a duk duniya, saboda haka wakilai mahalartan shawarwarin cinikayya na kasashe masu tasowa da yawa sun halarci taron. Da Malama Li Xuan, babban masanin ilmin tattalin arziki ta cibiyar kudu ta tabo magana a kan makasudin wannan taro, sai ta bayyana cewa, "wannan ne karo na farko da kasashe masu tasowa suka shirya taron tattaunawa a kan aiwatar da ikon mallakar ilmi. Bisa matsayinta na kungiyar gwamnatocin kasashe masu tasuwa, cibiyar kudu ta shirya wannan taron tattaunawa, domin taimakawa kasashe masu tasowa wajen magance matsi da ake yi musu a fannin kare ikon mallakar ilmi, da kuma binciken hanyar da za a bi don amfana wa kasashen masu tasowa wajen yin kirkire-kirkire da bunkasa harkokin tattalin arziki."

Yayin da mahalarta taron ke bayar da jawabai, sun nuna cewa, yanzu an riga an shiga zamanin tattalin arziki na ilmi a duk duniya. Malam Sun Zhenyu, jakadan kasar Sin a kungiyar cinikayya ta duniya shi ma ya bayar da jawabi inda ya ce, ya kamata, kasashe masu tasowa su shigar da aikin kirkirawa, da na kiyaye ikon mallakar ilmi cikin manyan tsare-tsarensu na bunkasuwa. Ya kara da cewa, "muna bukatar samun ikon mallakar ilmi, da yin amfani da shi da kula da shi da kuma kiyaye shi, ta yadda za mu kara kwarewa wajen samun sabuwar fasaharmu. Sa'an nan mu shigar da sabbin abubuwan kirkirawa cikin kasuwanni daga dakunan gwaji da cibiyoyin nazari, ta yadda za mu bunkasa tattalin arzikin kasashenmu ta hanyar kirkirawa ba cikin dogara da albarkatu ba."

1 2