Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-09 17:13:54    
Wuraren yawon shakatawa 3 a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin na Yunnan na kasar Sin

cri

In an kwatanta shi da wurin yawon shakatawa na Dashilin, duwatsun da aka samu a wurin yawon shakatawa na Xiaoshilin sun yi kanana kadan. Bangon duwatsu na raba wannan wuri zuwa wasu lambuna. Yanzu an ajiye fitilu a wurin, in mutane na yawo a nan da dare, suna iya ganin duwatsu masu ban mamaki da siffofi daban daban a karkashin hasken fitilu.

A arewancin shiyyar yawon shakatawa ta Shilin wato yanki mai dimbin duwatsu, akwai wani wurin yawon shakatawa mai suna 'Naigu'. Ma'anar Naigu a harshen Sani na kabilar Yi ita ce tsoho da mai launin baki. Baya ga bakaken dogayen kusoshin duwatsu, akwai ramuka a karkashin kasa, shi ya sa an sami kyan karkara na tsarin yanayin kasa na Karst mai ban mamaki a wajen, wato yana kasancewa da dimbin duwatsu a kan kasa tare da ramuka a karkashin kasa a wurin yawon shakatawa na Naigu. Malama Briana Lopez, 'yar kasar Australia ta nuna babban yabo kan manyan duwatsun da ta gani a wurin yawon shakatawa na Naigu, ta ce, 'Suna da matukar ban mamaki, siffofin wadannan duwatsu na da kyan gani kwarai da gaske.'

Ban da wannan kuma, kusoshin duwatsu da aka samu a shiyyar wurin yawon shakatawa na Shilin kan canza launinsu bisa yanayi, wato in ana ruwa, launinsu kan canza zuwa baki daga fari, in an dauke ruwa, kuma launinsu ya koma fari.

A idanun mutane, ga alama ba su fahimci kyaun shiyyar yawon shakatawa na Shilin wato yanki mai dimbin duwatsu ba har abada, haka kuma ba su iya sifanta kyan ganinta da kalmomi ba. A idanunsu kuma, kyan ganin wani kusar dutse da wani wurin yawon shakatawa a wajen ya kan sha bamban a yanayi daban daban, ko yanayin sararin sama daban daban, har ma a lokuta daban daban na wata rana.


1 2