Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-09 17:13:54    
Wuraren yawon shakatawa 3 a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin na Yunnan na kasar Sin

cri

A gun babban taron kayayyakin tarihi na kasa da kasa a karo na 31 da aka yi a birnin Christchurch na kasar New Zealand a watan Yuni na wannan shekara, wurare masu tsarin yanayin kasa na Karst da ke kudancin kasar Sin da suka hada da yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin na lardin Yunnan da sauran wurare 2 na kasar Sin sun sami nasarar shiga takardar sunayen kayayyakin tarihi na kasa da kasa bayan da aka dudduba rokonsu da kuma kada kuri'a, ta haka sun zama na 34 a kasar Sin a matsayin kayan tarihi na duniya.

Yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin na cikin gundumar Shilin ta kabilar Yi mai cin gashin kanta ta birnin Kunming na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, nisan da ke tsakaninsa da Kunming, babban birnin lardin Yunnan ya kai misalin kilomita 78. A cikin wuri mai fadin murabba'in daruruwan kilomta, an samu dimbin duwatsu manya da kanana a gangarar tsaunuka da kwaruruwa. Malama Bi Yunhua, mai jagorantar masu yawon shakatawa ta bayyana cewa, 'Fadin shiyyar yawon shakatawa na Shilin ya kai misalin murabba'in kilomita 12, shi ne wuri mai tsarin yanayin kasa na Karst mafi fadi a kasarmu har ma a duk duniya. A galibi dai masu yawon shakatawa na iya kallon manya da kananan yankuna masu dimbin duwatsu a lokacin da suke yawo a wajen. A shiyyarmu akwai duwatsu masu yawa da kananan hanyoyi fiye da 400 da kuma wuraren yawon shakatawa fiye da 200, shi ya sa ake kiranta wuri mai dimbin hanyoyi masu rikitaswa a karkashin gadon teku.'

Wurin yawon shakatawa na Dashilin yana tsakiyar shiyyar wurin yawon shakatawa ta Shilin, ya fi nuna sigar musamman ta wannan shiyya, wato tsarin yanayin kasa na Karst, tarihinsa kuma ya fi tsawo.

Rumfar Wangfeng wuri ne mafi kyau wajen kallon wadannan dimbin duwatsu. A idon madam Ni Ni,'yar birnin Shanghai, ta ji mamakin duniya bisa yayin da take kai ziyara a wannan yanki mai dimbin duwatsu. Ta ce, 'Daga rumfar Wangfeng, na hango dimbin duwatsu a kasa, wannan na da kyan gani sosai. Ina tsammani cewa, duniyarmu wuri ne mai ban mamaki. Yanayin halittar muhalli ne ya samar mana da karkara mai kyau.'

Wurin yawon shakatawa na Dashilin na hade da dimbin manyan duwatsu. In wani yana yawo a wajen, ya kan gamu da manyan duwatsu a cikin gajeren zango. Wadannan manyan kusoshin duwatsu na da ban mamaki sosai, wasu sun yi kama da mutane, wasu kuma sun yi kama da wasu abubuwa daban. Malama Bi ta gaya mana wani abu mai ban sha'awa, wato a cikin shiyyar yawon shakatawa ta Shilin, wasu duwatsu ana iya kallonsu, wasu kuma ana iya taba su, wasu kuwa na iya samar da kara mai ban mamaki bayan da aka buge su.

1 2