Dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na kasar Sin dakin nune-nunen kayayyakin fasaha ne mafi girma a duk kasar Sin, shi ne daya daga cikin manyan gine-gine 10 da aka gina su don murnar cikon shekaru 10 da kafuwar Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, mazauninsa na arewa maso gabashin fadar sarakuna ta kasar Sin wato Forbidden City a birnin Beijing, hedkwatar kasar, wanda ke dora muhimmanci kan nuna da ajiye da kuma nazarin kayayyakin da masu fasaha na zamani da zamanin kusa da na yanzu na kasar Sin, sa'an nan kuma wuri ne na matsayin koli wajen nuna kayayyakin fasaha na kasar Sin, shi ya sa ya ba da babban tasiri a rukunin fasaha.
An fara gina babban ginin wannan dakin nune-nunen kayayyakin fasaha kamar irin dakin gargajiya na kasar Sin tun daga shekarar 1958, an gama gina shi a shekarar 1962. Dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na kasar Sin ya nuna salon kabilu na gargajiya sosai. Shehun malami mai ilmin gine-gine Mr. Dai Nianci ne ya jagoranci zana wannan dakin nune-nunen kayayyakin fasaha, ya koyi salon gine-gine na kogon dutse na Mo Gao Ku da ke Tunhuang, ya ci nasarar hada salon gine-gine na zamani da na kabilu gaba daya wajen zana wannan dakin nune-nunen kayayyakin fasaha. Fadin dakin nune-nunen kayayyakin fasahar nan ya kai murabba'in mita misalin dubu 30, fadin babban gininsa ya kai murabba'in mita dubu 17 da 51, jimlar fadin dakunan nune-nunen kayayyakin fasaha guda 14 ta kai murabba'in mita dubu 6.
1 2
|